Cikin hawaye: An binne gawar shugaban KASTLEA da ya mutu a Kaduna

Cikin hawaye: An binne gawar shugaban KASTLEA da ya mutu a Kaduna

A ranar Litinin ne aka binne gawar kanal Jackson Tinat Zamani (mai ritaya), tsohon shugaban hukumar tabbatar da bin dokokin tuki ta jihar Kaduna (KASTLEA).

'Yan uwa da abokan arzikin marigayin sun hallara cikin hawaye da juyayi a yayin da aka binne shi a makabartar 'Commonweath War Commentary' da ke Kaduna.

An ga abokai da dangin marigayi Zamani na zubar da hawaye a makabartar da aka binne shi. Sun bayyana marigayin a matsayin mai kirki, son zaman lafiya, da kaunar al'umma.

Marigayi Kanal Zamani ya mutu ne a ranar 30 ga watan Yuni, 2019, bayan ya sha fama da rashin lafiya. Ya mutu ya na da shekaru 60 a duniya.

DUBA WANNAN: Cikin hawaye: An binne gawar shugaban KASTLEA da ya mutu a Kaduna

Ya mutu ya bar matarsa, Henrieta Obiageli Zamani, da 'ya'ya hudu; Talatu Philomena Henry, Gimbiya Akintunde, Frederick Akut Zamani da Amina Zamani da jikoki da dama.

An haifi marigayi Zamani a ranar 15 ga watan Maris a shekarar 1954 a karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.

Ya yi karatun firamare a Jankasa kafin daga bisani ya wuce zuwa makarantar sojoji ta Zaria daga shekarar 1969 zuwa 1973. Ya kammala karbar horon aikin soja a shekarar 1975.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel