To fah: An nemi a hallaka saurayin nan da ya angwance ta shafin Facebook a Kano

To fah: An nemi a hallaka saurayin nan da ya angwance ta shafin Facebook a Kano

- Saurayin nan da yayi aure ta shafin Facebook a Kano ya nuna fargabar sa

- Inda ya ce yana tsoron abinda zai iya biyo, yayin da wasu matasa suka kai masa hari, suka ji masa ciwo

- Sannan bayan haka ana ta turo masa sakonni na barazana ga rayuwarsa ta wayar salula

Saurayin nan, wanda ya shiga hannun hukumar Hisbah ta jihar Kano, ya bayyana cewa wani matashi ya kai masa hari, inda har ya ji masa ciwo a hannu, akan auren da yayi na Facebook.

Tun lokacin da aka daura auren, maganar ta yadu a shafukan sada zumunta, hukumar shari'a ta jihar Kano ta bayyana cewa auren ya sabawa shari'ar addinin musulunci, kuma za ta hada kai da hukumar Hisah ta jihar domin a hukunta saurayin da duk masu hannu a wannan lamarin.

Matasan guda hudu wadanda ake zargin suke da hannu a wannan lamarin, sun bayyana kansu a gaban hukumar, inda kowanne daga cikinsu ya nuna dana sanin aikata wannan lamari.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya yiwa wani manjo janar karin girma zuwa mukami daya da na Buratai

Shugaban hukumar Hisbah na jihar, Malam Abba Saidu Sufi ya bayyana cewa sun saurari maganganun matasan, sannan kuma sun yi musu nasiha, inda angon da abokanansa suka amsa laifinsu sannan suka yi nadamar abinda suka aikata.

Shugaban ya ce nan ba da jimawa ba hukumar za ta san matakin da zata dauka akan matasan guda hudu.

Sannan kuma hukumar ta yi Allah-wadai da harin da aka kaiwa matashin, sannan ta bukaci hukumar 'yan sanda ta dauki mataki akan lamarin.

A makon da ya gabata ne dai maganar auren shafin Facebook din ta fito fili, yayin da wani saurayi mai suna Sanusi Abdullahi dake jihar Kano ya bayyana cewa shi da wata budurwa dake Maiduguri jihar Borno mai suna Zainab, da wasu abokanansa suka daura musu aure.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel