Tirkashi: Munanan abubuwa guda 12 da iya 'yan arewa ne kawai suke yi a Najeriya - Fani Kayode

Tirkashi: Munanan abubuwa guda 12 da iya 'yan arewa ne kawai suke yi a Najeriya - Fani Kayode

- Tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Fani Kayode ya bayyana wasu munanan abubuwa guda sha biyu da 'yan arewa suke yi

- Ya bayyana hakan ne a wani martani da yake mayarwa da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai bayan yayi maganar cewa duka arewa babu wanda aka taba kamawa da laifin damfara ta yanar gizo

- Tsohon ministan ya bayyana cewa, arewa ce cibiyar shaye-shaye, ta'addanci, kashe-kashe, kabilanci, garkuwa da mutane da sauransu

Tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Fani Kayode, ya bayyana wasu munanan abubuwa guda sha biyu da iya 'yan arewa ne kawai suke yi a kasar nan.

Fani Kaoyde ya bayyana wadannan abubuwan ne a wani martani da yake mayarwa da gwamnan jihar Kaduna Malam Ahmed El-Rufai, bayan gwamnan ya bayyana cewa ba a taba kama dan arewa da laifin damfara ta yanar gizo ba.

KU KARANTA: Babbar magana: Nan da shekara 20 matasan arewa zasu koma shara da wanke-wanke saboda rashin ilimi - Sarki Sanusi

Ga jerin munanan abubuwan da ya lissafo guda 12:

1. Shaye-shaye

2. Ta'addanci

3. Garkuwa da mutane

4. Kabilanci

5. Ci da addini

6. Kisan gilla

7. Bangaranci

8. Kashe-kashe

9. Wariyar addini

10. Kyamar kiristoci

11. Fyade

12. Fada da mataye

A karshen satin da ya gabata ne dai gwamnan Kadunan yayi maganar cewa ba a taba kama dan arewa da laifin damfarar yanar gizo ba, ma'ana (Yahoo-Yahoo).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel