Jami'an kwastam sun kama kwantaina 42 makare da kwayar 'Tramol'

Jami'an kwastam sun kama kwantaina 42 makare da kwayar 'Tramol'

Ofishin hukumar hana fasa kwabri ta kasa (kwastam) reshen Apapa a jihar Legas ya sanar da cewa ya kama wasu kwantainoni guda 42 makare da kwayar 'Tramadol' da aka shigo da ita daga wata kasar waje.

Mohammed Abba Kura, shugaban ofishin kwastam na Apapa, ne ya bayyana hakan yayin magana da manema labarai a ranar Talata. Ya ce jami'an kwastam sun kama wasu karin kwantainoni 24 na wasu haramtattun kaya da aka shigo da su Najeriya.

"Irin wadannan kaya sun hada da tumaturin gwangwani, man girki, takalma da kayan kwalliyar mata, tramol da sauran kwayoyi", a cewar Kura.

Ya kara da cewa sun kama wasu gilasai masu garkuwa da kayan haka rami da ke dauke da wasu rubutu na yaren kasar waje. Kura ya ce dukkan kayayyakin sun saba wa dokar hana shigo da kaya da aka sabunta a shekarar 2018/2019.

DUBA WANNAN: Yadda wata amarya ta mutu ranar daurin aurenta bayan ta amsa kiran waya

"Mun kama wasu mutane da ke da hannu a cikin shigo da haramtattun kayan. Har yanzu mu na gudanar da bincike kafin mu gurfanar da su," a cewar sa.

Kazalika, ya bayyana cewa ofishinsu na Apapa ya karbi kudin shiga da yawansu ya kai biliyan N203 daga watan Janairu zuwa Yuni na shekarar 2019.

"kudin da muka samu ya kai kaso 54.5% na jimillar kudin da ake saka ran za mu samar a cikin shekarar nan.

"Mun samu karin kudin da yawansu ya kai N26,507,298.24 idan aka kwatanta da muka samu daga watan Janairu zuwa Yuni na shekarar 2018," a cewar Kura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel