Hadin kai ne kadai zai kawo karshen rashin tsaro da kabilanci a Najeriya - Osinbajo, Tinubu

Hadin kai ne kadai zai kawo karshen rashin tsaro da kabilanci a Najeriya - Osinbajo, Tinubu

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo tare da babban jigo na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, sun yi kira na tabbatar da hadin kai a tsakanin al'ummar kasar nan a matsayin mafificiyar hanya ta magance rashin tsaro da kuma kabilanci da suka addabi kasar nan.

Kusoshin biyu na jam'iyya mai ci ta APC sun bayyana wannan ra'ayi a wurin bikin kaddamar da wani littafi yayin murnar cikar tsohon gwamnan jihar Ogun shekaru 80 a duniya, Cif Olusegun Ogbah da aka gudanar a jihar Legas.

A yayin taron da manyan kasar nan suka halarta kama daga tsaffin gwamnoni, ministoci, da kuma gwamnonin yankin Kudu maso Yamma, Osinbajo ya jaddada muhimmancin hadin kai domin yaye annobar kabilanci da ta mamaye zukatan al'ummar kasar nan.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana ta'addanci a matsayin wata muguwar masifa da ba ta bambamce tsakanin kabilu, addini ko kuma akida ta siyasa. Ya ce dole al'ummar Najeriya su hada kawunan su wuri guda domin tabbatar da samun kyakkyawar makoma.

KARANTA KUMA: Ikon Allah ne kadai ya sanya na samu mukamin sakataren gwamnatin Tarayya - Boss Mustapha

Babban taron da ya gudana a Otel din Eko dake unguwar Victoria Island ya samu halarcin manyan kasar nan da suka hadar da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan, gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson da kuma takwaransa na jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hadar da Abdulsalami Abubakar, Femi Pedro, Prince Dapo Abiodun, Oba Rilwani Akiolu, mataimakin gwamnan jihar Legas, Obafemi Hamzat, Abiola Ajimobi, Bisi Akande, Otunba Gbenga Daniel, Kayode Fayemi, Donald Duke da sauransu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel