Wata sabuwa: An yi mun barazana ne yasa dole nasa hannu a sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 - Mohammed Tata

Wata sabuwa: An yi mun barazana ne yasa dole nasa hannu a sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 - Mohammed Tata

- Wani shaida da jam'iyyar PDP da Atiku suka gabatarwa kotun zabe, ya bayyana cewa an tilastashi ne shi yasa ya sanya hannu a sakamakon zaben shugaban kasa na 2019

- Ya bayyana cewa an yi masa barazanar za a rabashi da aikinsa na N-Power ne idan bai sanya hannu ba

- Ya bayyana cewa yanzu haka yana nan yana aikin shi saboda sanya hannun da yayi

Mista Mohammed Tata, wanda shine mutum na biyar da Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP suka gayyato a matsayin shaidan su a kotun shari’ar zaben shugaban kasa, ya shaidawa kotu cewar; tilasta shi aka yi ya sanya hannu a sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 a jihar Jigawa.

“An yi mun barazana gami da tsoratar da ni domin in sa hannu a sakamakon zaben shugaban kasa, sannan aka gaya mun cewar idan ban sanya hannu ba za’a cire suna na a cikin ma’aikatan N-power.” Inji Mohammed Tata.

Da aka yi masa tambaya, ko bai aminta cewa shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC sun sami kuri’a 700 ba ne a akwatin sa, Mohammed yace “Ai babu alkalumman zabe domin ba’a ma yi zabe a wajen ba.”

Tata, ya kara da cewar “Ni musulmi ne, na yi imani da kaddara kuma duk abinda yaso ya faru shi zai faru, ko PDP ta yi nasara ko APC tayi nasara ba ni da matsala da wannan, abinda nake bukata kawai shine ayi shari’ar adalci a kasa ta.”

KU KARANTA: Ke Duniya: Wallahi ina neman wacce zanyi lalata da ita ne - Abinda wani gardi ya ce kenan yayin da aka kama shi a dakin mata na FCE Kano

“Ban damu da nasarar jam’iyya ko faduwar ta ba, amma dai ban ji dadin abinda ya faru ba.” Cewar Mohammed Tata.

Da aka sake tambayar Mohammed Tata, ko an bashi kwafin sakamakon zaben, sai yace “A’a ba’a bani ba saboda rigima babu zaman lafiya a wajen.”

“Na bi duk hanyoyin da suka dace wajen kai rahoton abubuwan da suka faru na barazanar da aka yi mun, amma ba’a hukunta wadanda suka aikata laifin ba.”

“Ban bayyana sunansu ba a cikin bayanai na saboda dalili na tsaro, anma dai har yanzu ina aiki da N-Power saboda na sanya hannu a sakamakon zaben, inda ban saka hannu ba da yanzu sun kore ni daga aiki na.” A cewar Mista Mohamed Tata shaidan Atiku da PDP a gaban kotun shari’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel