Babbar magana: Nan da shekara 20 matasan arewa zasu koma shara da wanke-wanke saboda rashin ilimi - Sarki Sanusi

Babbar magana: Nan da shekara 20 matasan arewa zasu koma shara da wanke-wanke saboda rashin ilimi - Sarki Sanusi

- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa nan da shekara ashirin yankin arewa zasu shiga cikin matsala da tashin hankali idan har basu hada kai ba

- Ya bayyana cewa nan da shekaru ashirin din, za a nemi likita ko soja, ko dan sanda a yankin arewa saboda tsabar rashin ilimi

- A karshe ya bayyana cewa dole 'yan arewa su tashi tsaye domin hada kai da kuma bai yara tarbiyya da ilimi mai amfani

A wani taro da aka gabatar a fadar Sarkin Kano, mai martaba Muhammad Sanusi II, Sarkin ya jawo hankalin al'ummar arewa akan hadin kai domin samun cigaba yankin.

Sannan kuma sarkin ya koka akan irin yadda yara kanana ke yawo lungu-lungu kwararo-kwararo basa zuwa makaranta domin koyar ilimi.

Ga bayanin mai martaba sarkin:

"Kullum abinda muke cewa, Kano dinnan da muke cin moriyarta muke jin dadi, muke kuma alfahari cewa mu 'yan Kano ne, wadansu ne suka gina ta. Kuma kowacce al'umma tana da hakki taga cewa ta kawo cigaba yadda 'yan baya zasu yi alfahari.

KU KARANTA: Wata sabuwa: An yi mun barazana ne yasa dole nasa hannu a sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 - Mohammed Tata

"Saboda haka abinda nake fata, mu dauki manyan matsaloli da suke fuskantarmu, irinsu talauci, rashin aikin yi da rashin ilimi, mu zauna mu hada kanmu muga yadda zamu warware wannan matsalolin.

"Kullum muna zancen yara da basa zuwa makaranta, wadannan yaran da suke yawo a titunan Kano, sa'o'insu a jihar Legas, Port Harcourt da sauran jihohi na kudancin kasar nan, duka suna zuwa makaranta, suna koyan lissafi, turanci, suna koyar yadda ake amfani da na'ura mai kwakwalwa.

"Nan da shekara ashirin za a zo ana neman masu karatu da zasu shiga aikin soja, dan sanda da sauransu, tunda yaranmu ba karatu ne dasu ba dole 'yan kudu za a dauka. Haka shiga jami'a, karatun aikin likita, idan aka je asibiti aka ga matashi dan arewa to ba zai wuce mai gadi ba ko mai share-share, amma wadanda suke aikin likitocin ba 'yan arewa bane.

"Saboda haka 'yankin arewa, idan bamu yi da gaske ba muna cikin tashin hankali da matsala nan da shekara ashirin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel