Shaidan Atiku da PDP ya basu kunya a gaban kotu

Shaidan Atiku da PDP ya basu kunya a gaban kotu

Audu Sani, mai bayar da shaida na 13 da Atiku Abubakar da jam'iyyar PDP ta gabatarwa kotun sauraron karar zaben shugaban kasa a ranar Talata ya fadawa kotu cewa ba zai iya tuna ranar da aka gudanar da zaben shugaban kasa da ta gabata ba.

Sani, wanda jami'in sanya idanu kan kidayan kuri'un zabe na jam'iyyar PDP ne a karamar hukumar Lapai na jihar Niger ya yi ikirarin cewa an samu hargistsi da harbe-harben bindiga da sassan mazabarsa wanda hakan ya hana yin zabe a yankin.

Shaidan ya bayyana ne gaban alkalai biyar karkashin jagorancin Justice Garba Usman domin bayar da shaida kan kallubalantar nasarar da shugaba Muhammadu Buhari ya samu a zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu a madadin jam'iyyar PDP da dan takarar shugaban kasar ta Atiku Abubakar.

DUBA WANNAN: An kama wasu mata 4 dumu-dumu suna madigo a Kwallejin Kimiyya a Kebbi

A yayin da ya ke amsa tambayoyi, ya ce ya mika sakamakon zaben (jimlan kuri'un) na karamar hukumarsa ga jami'in kidaya na jam'iyyarsa.

A yayin da lauya mai kare jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Lateef Fagbemi (SAN) ya tambaye shi ranar da ya mika sakamakon zaben, ya ce ya mika ne a ranar 26.

Da aka tambaye shi ko wane wata ne, sai ya ce '26 ga watan Afrilu.'

Da aka tambaye shi ranar da aka yi zaben sai ya ce ranar '23'

Amma da aka bukaci ya bayyana watan sai ya ce, 'ba zan iya tunawa ba'.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel