Zanga-zangar yan Shi’a na barazana ga zaman lafiya da tsaron birnin tarayya – Mazauna yankin

Zanga-zangar yan Shi’a na barazana ga zaman lafiya da tsaron birnin tarayya – Mazauna yankin

Al’umman babbar birnin tarayya sun bayyana ayyukan kungiyar yan Shi’a a Abuja a matsayin abun damuwa kuma hakan na iya zama barazana ga kwanciyar hankali da tsaron yankin.

Sun bukaci hukumomin tsaro da su gargadi kungiyar, su kuma tabbatar da tsaron mutanen birnin.

Tun daga lokacin da aka rufe El-Zakzaky, Shugaban kungiyar Shi’a, mabiyansa na ta kaddamar da zanga zanga a wasu sassa na biranen kasar ciki har da babban birnin tarayya inda suka bukaci a saki shugaban su.

Lamarin ya kan kasance tare da datse hanyoyi a babbar birnin wanda hakan na janyo rashin jin dadin yawancin al’umma a lokacin aiki.

A Oktoban 2018, yan sanda sun kama mambobin kungiyar 400 bayan sun gudanar da zanga zanga a babbar birnin tarayya.

An kwace makamai masu hatsarin gaske daga hannun wasu mambobin kungiyar.

Al’umma sun kasance cikin damuwa cewa ci gaba da zanga zangan da kungiyar ke zai saka birnin da al’ummanta cikin hatsari.

KU KARANTA KUMA: Wata matashiya Asmau Haruna ta bata bayan ta bar gidansu a Kaduna zuwa Kano

Al’umma na son kungiyar ta natsu su kuma yi hattara da saka rayukan matafiya a hatsari.

An kama Shugaban kungiyar, Ibrahim El-Zakzaky a 2015 bayan mambobinsa sun tunkari ayarin motocin Shugaban rundunan Soji a Zaria.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel