Buhari ya bukaci majalisar ta amince da nadin Farfesa Galadima a matsayin shugaban NIPSS

Buhari ya bukaci majalisar ta amince da nadin Farfesa Galadima a matsayin shugaban NIPSS

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci majalisar dattijai ta amince da nadin Farfesa Habu Galadima a matsayin sabon babban darektan cibiyar horon manyan jami'an gwamnati (NIPSS) da ke Kuru, a Jos, jihar Filato.

Shugaban majalisar dattijai, Dakta Ahmad Lawan, ne ya karanta wasikar da shugaban kasar ya aiko zuwa majalisar yayin zaman ta na ranar Talata.

Buhari ya ce sashe na 8 (5) na dokokin NIPSS ne ya bashi ikon rubuta wasikar da ya aika wa majalisar a ranar 9 ga watan Yuli.

Ya bukaci mambobin majalisar su bashi hadin kai wajen tabbatar da nadin Farfesa Galadima a matsayin shugaban NIPSS ba tare da wata matsala ba.

Shugaban kasar ya hada da takardun Farfesa Galadima da ke dauke da irin karatun da ya yi da kuma gogewarsa a aiki da kuma dukkan wasu bayanai da zasu taimaka wa majalisar wajen tantance shi.

DUBA WANNAN: Yadda wata kyakyawar budurwa ta mutu ranar auren ta bayan amsa kiran waya

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa an haifi Galadima a shekarar 1963 a karamar hukumar Toto da ke jihar Nasarawa.

Yanzu haka Galadima farfesa ne a fannin kimiyyar siyasa a jami'ar Jos, jihar Filato, inda ya yi karatun digirinsa na farko; a shekarar 1987, da na biyu(MSc); a shekarar 1990, da na uku (PhD); a shekarar 2006.

Farfesa Galadima ya rike shugaban sashen karatun kimiyyar siyasa a jami'ar Jos, sannan ya taba aiki da kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) da bankin duniya da wata kungiyar majalisar dinkin duniya (UNDP)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel