Saurayi dan shekara 14 ya shiga hannu da laifin fyade a kasar Jamus

Saurayi dan shekara 14 ya shiga hannu da laifin fyade a kasar Jamus

A ranar Litinin 8, ga watan Yuli, wani saurayi mai shekaru 14 a duniya, ya shiga hannun hukumar 'yan sanda da laifin keta haddin wata matashiyar mata da ya yi mata fyade a kasar Jamus dake nahiyyar Turai.

Jami'i mai shigar da kara, ya ce hukuma ta kai hannu kan wannan saurayi domin fargaba ta yiwuwar sake aikata wannan mummunan laifi a karo na gaba.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, saurayin da ake zargi ya yi kaurin suna biyo bayan aikata wannan muguwar ta'asa karo da dama tun gabanin hukuncin doka ya fara aiki a kansa. Sai dai a yanzu dokar kasar Jamus za tayi aiki a kansa yayin da ya kai shekaru 14 na haihuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan saurayi na daya daga cikin mutane biyar da ake zargi da zakkewa wasu mata biyu 'yan shekaru 14 da kuma wasu matan biyu 'yan shekaru 12 wanda dukkanin su sun kasance 'yan asalin kasar Bulgaria.

Kazalika, ana kuma zargin samarin biyar da laifin zakkewa wata budurwa ta karfin tsiya mai shekaru 18 a ranar Juma'a ta makon jiya. Mamuguntan sun danne wannan budurwa a bayan wani fegi dake yankin Mulheim a Arewacin garin Wesphalia na kasar Jamus.

KARANTA KUMA: Wani Mutum ya yi garkuwa da surukin sa mai shekaru 88 a jihar Imo

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan jaridar Legit.ng ta ruwaito, wani Limamin addinin kirista ya shiga hannun hukuma, biyo bayan kama sa da laifin yiwa wata budurwa mai shekaru 15 fyade da har rabo ya fada na samun juna biyu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel