Da zafinsa: ‘Yan majalisa 14 na Edo sun tunkari Majalisar dokoki da neman a sake zaben shugabancin majalisar jiharsu

Da zafinsa: ‘Yan majalisa 14 na Edo sun tunkari Majalisar dokoki da neman a sake zaben shugabancin majalisar jiharsu

-Yan majalisar Edo sun dira majalisar dokokin tarayya da neman a sake gudanar da zaben shugabannin majalisar jiharsu

-Daga cikin mambobin 14 akwai kanin shugaban jam'iyyar APC na kasa Seid Oshiomole wanda suka tsira da kyar daga hannun yan daba a wani otal a Benin

‘Yan majalisa 14 da suka fito daga jihar Edo sun dira Majalisar dokoki da neman a sake gudanar da sabon zaben shugabancin majalisar jihar Edo.

Kwamaret Peter Akpatason da Farfesa Julius Ihonvbere wadanda ke majalisar wakilai ne ake sa ran zasu mika kudurin cewa majalisar dokoki ta karbe ragamar majalisar domin sake yin zaben shugabannin wannan majalisarta Edo.

KU KARANTA:Mutumin da matarsa ta dabawa wuka ya samu lafiya, ya nunawa bidiyon tsairaci da matarsa ke tura wa samarinta

Idan baku manta ba, ‘yan majalisar su 14 sun bar jihar Edo ne a sakamakon farmakin da ‘yan daba suka kai masu a wani otal dake Benin inda suka lakada masu dukan tsiya cikinsu hadda Mista Seid Oshiomole kanin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Har ila yau, a cikin 'yan kwanakin da suka gabata ne rikici ya barke Majalisar jihar Edo inda ta kasance an samu rudani sakamakon zaben shugabannin majalisar.

Lamarin wanda a cewar shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomole ya samo asali ne a sanadiyar wasu jiga-jigai a siyasar jihar Edo masu fada a ji.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel