Yanzu Yanzu: Buhari, Baru da Kyari sun gana a Aso Rock

Yanzu Yanzu: Buhari, Baru da Kyari sun gana a Aso Rock

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 9 ga watan Yuli yayi ganawar sirri tare da sabon Shugaban kamfanin man fetur din Najeriya da kuma tsohon Shugaban kamfanin a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Sun fara ganawar ne da misalin 11:30 na safe a ofishin Shugaban kasa.

Male Kolo Kyari ya karbi mulki daga hannu Maikanti Baru a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli a matsayin manajan darakta na NNPC na 19.

Su biyun sun isa fadar Shugaban kasa da misalin 11:05 na safe.

Baru yayi ritaya daga aikin kamfanin a ranar 7 ga watan Yuli bayan ya cika shekara 60 a duniya wanda shine shekarun ritaya daga aikin gwamati.

Kafin nadinsa, Kyari ya kasance Janar Manaja na sashin tallata danyen main a NNPC.

KU KARANTA KUMA: Elisha Abbo: Hadimar Buhari tace lallai sai dai a tura sanatan gidan yari

Ya kuma kasance wakilin Najeriya a kungiyar OPEC tun 2018.

A lokacin da ya karbi mulki, Mele ya sha alwashin aiki da gaskiya tare da bunkasa ma'aikatar man fetur din, sannan ya sha alwashin farfado da ma'aikatu hudu na man fetur.

Har yanzu suna kan ganawa da Shugaban kasar a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel