Yanzu-yanzu: Atiku ya lallasa Buhari a Katsina - Wani shaida ya laburtawa kotun zabe

Yanzu-yanzu: Atiku ya lallasa Buhari a Katsina - Wani shaida ya laburtawa kotun zabe

Shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP na jihar Katsina, Salisu Maijigri, ya bayyanawa kotun zaben shugaban kasa ranar Talata cewa dan takarar kujeran shugaban kasa jam'iyyar, Atiku Abubakar, ya lallasa shugaba Buhari a jihar.

Atiku da jam'iyyarsa, sun shigar da kara kotun zabe karkashin jagorancin Alkali Mohammed Garba, inda suka kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar All Progressives Congress APC.

A yau Talata da kotun ta dawo zama, jam'iyyar PDP ta gabatar da shaidanta na takwas, Maijigiri, wanda ya kasance wakilin jam'iyyar a cibiyar tattara zaben shugaban kasa a jihar Katsina.

KU KARANTA: Mahaifina zai mutu idan ba'a dau mataki ba - Dan El-Zakzaky

Yayinda ake yi masa tambayoyi, Maijigiri ya ce sabanin sakamakon da hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta sanar, sakamakon da suka tattara da kansu ya nuna cewa jam'iyyar APC ta samu kuri'u 872,000 yayinda PDP ta samu 905,000.

Sakamakon da hukumar INEC ta sanar shine cewa jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 160,203 yayinda APC ta samu 1,505,633.

Yace: "Mu (PDP) ne muka samu nasara ba APC ba. APC ta samu kuir'u 872,000 kuma PDP ta samu 905,000."

"Wadannan sune sakamakonmu, mu muka tattara su a jiharmu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel