Na yi danasanin rashin mika mulki ga dan takarar da na so – Tsohon gwamna Yari

Na yi danasanin rashin mika mulki ga dan takarar da na so – Tsohon gwamna Yari

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari, ya bayyana bangarori biyu da yayi danasani watanni biyu bayan barinsa kujerar mulki.

Sai dai kuma Yari, ya bukaci mazauna jihar da su marawa gwamnati mai ci baya koda dai jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ce ke jagoranci a yanzu.

Yari wanda, yayi Magana a wata hira da jaridar Nigerian Tribune, yace ya dauka cewar zai mika mulki ga mutumin da ya fahimci tafiyar siyasarsa sannan kuma wanda zai ci gaba daga inda ya tsaya.

“Na dauka zan mika mulki ga wanda ya san inda na tsaya kuma wanda zai cigaba daga inda muka tsaya a matsayinmu na jam’iyyar siyasa. Amman Allah da ikonsa, hakan bai faru ba.

“Na bar ayyuka da dama wadanda nayi yunkurin kammalawa kamar jami’ar jihan. Na so aikin jami’an ta kammalu zuwa kashi 60 zuwa 70 saboda idan sabon gwamnati ta shigo ta kammala sauran aikin.

“Hanyar Anka-Bagega yana daga cikin sauran ayyukan da na so ace na kammala, amman aikin bai kammalu ba saboda rashin kudin da jihar ta fiskanta."

Da aka tambaye shi: ‘A 2011 a lokacin da ka karbi mulki, ayyuka nawa ne gwamnatinka ta gada daga gwamnatin da ya gabata?’

Yari yace: “A lokacin da na karbi mulki, na sami ayyuka daban daban fiye da 480 wadanda ba a kammala ba, wassu ayyukan sun kai matakin kashi 20, wassu sun kai kashi 30 yayin da kadan ne suka kai kashi 60 . A lokacin da mulkina ke zuwa karshe, nayi zatton zan mika mulki ga wanda zai tabbatar da cigaba.

“Rashin tsaro ya kasance mafi tsananin lamari dake kalu balantar Zamfara. Yaya kaji a lokacin da ba bar mulki ba tare da maganta lamarin yan bindiga ba a jihan?

“Na gaji matsalar tsaron Zamfara kuma ban taba fatan barin mulki ba tare da naa magance matsalar ba. Saboda haka, an kashe makudan kudade a kokarin ganin an magance lamarin tsaro. Na san an rasa rayuka da dama tare da hasarar kaddarori sanadiyyan rashin tsaro.

“Rashin tsaro yana daya daga ciki abubuwan da na gaza magancewa, duk da makudan kudaden da gwamnatina ta kashe.

“Kwarai da gaske, ina kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su baiwa gwamnatin yanzu goyon bayan da take bukata don kawo karshe matsalar yan bindiga a jihar.

“Har ila yau ina roko ga mutane da su hada kai tare da hukumomin tsaro su bada goyon baya ga manufofin da gwamnati ta shimfida don magance rashin tsaro a jihar da Najeriya gaba daya. Muddin babu tsaro ga rayuka da kaddarori, bana tsammanin za a samu cigaba mai amfani ba."

KU KARANTA KUMA: Boko Haram sun kashe sojoji 5 a Borno

Da aka tambaye shi cewa ‘Wani sako kake da shi zuwa ga mambobin jam’iyyanka, wanda ya zama tamkar jam’iyyar adawa a Zamfara?’

Gwamnan yace: “Zuwa ga magoya bayanmu masu hadin kai, ina son ku sani cewa ya kamata mu hada kai mu goyi bayan gwamnati mai ci, ba tare da la’akarin banbancin jam’iyya ba.

“Mu goyi bayan wannan gwamnatin don cigaban jihar Zamfara.

“Har ila yau zan yi amfani da wannan damar in karfafa cewa jam’iyyar APC reshen jihar zata taka rawanta na jam’iyyar adawa kwarai da gaske ga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai mulki.

“Jam’iyyar APC a matsayin jam’iyyar adawa zata samar da korafe-korafen da zai taimaki gwamnatin da PDP ke jagoranta wajen gudanar da ayyuka don cin amfanin damokardiyya ga mutane.

“Zamu yi korafe korafe ne akan abunda muka gani, mai ma’ana da kuma adalci, ba korafe korafen da zasu nuna batanci ba.

“Siyasar Zamfara yana kama da hadin kai da ake samu a cikin iyali, ko da yake muna da banbancinmu da muka warware da wadanda bamu warware ba.

“Daga karshe, zamu hada kanmu don gina jam’iyya mai karfi kafin siyasar 2023.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel