Boko Haram sun kashe sojoji 5 a Borno

Boko Haram sun kashe sojoji 5 a Borno

Kungiyar yan ta’addan Boko Haram sun kai wa sojojin Najeriya harin bazata a yankin arewa maso gabashin kasar, inda suka kasha akalla sojoji biyar sannan suka raunata sama da dozin guda, Reuters ta ruwaito.

Majiyoyi sun bayyana cewa akwai yiwuwar a samu Karin wadanda suka mutu domin har yanzu ba a ga wasu sojoji ba bayan harin a ranar Alhamis a Damboa, da ke jihar Borno.

Sojoji sun je yankin domin kakkabe wani sansani na Boko Haram, amma sai aka far masu a harin bazata, cewar majiyoyin.

Yan ta’addan Boko Haram sun kashe dubban mutane sannan sun mayar da miliyoyin mutane marasa galihu a Najeriya a tsawon lokacin da suka kwashe suna kai hare-hare.

Babban kwamandan rundunar, Birgediya Janar Bulama Biu, ya tabbatar da arangamar a tsakanin dakarun soji da yan Boko Haram, amma yace babu wanda ya mutu a bangaren sojojin.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun baje kolin wani makashin yar bautar kasa

Wasu majiyoyin sojoji uku da mayakan CJTF uku, sunce an gano gawarwakin sojoji biyar, da na mayaka 16, sannan sojoji 14 da yan farar hula biyu sun ji rauni. Majiyoyin sunce har yanzu ba a ga wasu mayakan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel