Wani Mutum ya yi garkuwa da surukin sa mai shekaru 88 a jihar Imo

Wani Mutum ya yi garkuwa da surukin sa mai shekaru 88 a jihar Imo

Cibiyar yaki da garkuwa da mutane reshen hukumar 'yan sandan jihar Imo, ta samu nasarar cafke wani matashi dan shekaru 29, EmManuel Sunday, bisa laifin kulla kutungwila da wasu mutane biyu wajen yin garkuwa da surukin sa mai shekaru 88 a duniya, Pa Njoku Louis.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya DCP Frank Mba ya bayyana yayin ganawa da manema labarai a ranar Lahadi, ya ce Emmanuel ya yi hadin baki da diyar dattijon mai shekaru 19, Chinaza Nwogu da kuma dan sa wajen aikata wannan muguwar ta'asa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, miyagun mutanen uku sun yi nufin amfani da kudin fansar wannan dattijon domin gudanar shagalin bikin Emmanuel da kuma Chinaza.

A halin yanzu Emmanuel da Chinaza da kuma wasu ababen zargi kimanin 19 sun shiga hannun hukumar 'yan sanda da laifukan fashin da makami, garkuwa da mutane da kisan kai kamar yadda bincike ya tabbatar.

KARANTA KUMA: Zan sake koma wa kujerar gwamnan jihar Bayelsa - Sylva

Kakakin 'yan sandan ya kuma yi karin haske dangane da yadda ababen zargin suka yi garkuwa da wata yarinya 'yar shekaru biyar, Deborah Chidinma Nganodim, da tuni sun karbe Naira miliyan 1.2 kudin fansar ta.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan jaridar Legit.ng ta ruwaito, rundunar dakarun sojin kasa ta samu nasarar kubutar da wasu fasinjoji 13 da suka afka tarkon masu garkuwa da mutane a kauyen Kuyelo na karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel