Yan sanda sun baje kolin wani makashin yar bautar kasa

Yan sanda sun baje kolin wani makashin yar bautar kasa

Rundunar yan sandan jihar Imo sun kama wani mutum mai suna Chukwuemeka Ezek an zargin fyade da kisan wata mace yar shekara 27, Lilian Mgbanwa, wacce ta kammala bautar kasarta.

Kakakin rundunar, Frank Mba ne ya gurfanar da Eze a ranar Litinin, a hedkwatar rundunar da ke Owerri, babbar birnin jihar.

Kakakin yan sandan ya fada wa manema labarai cewa an kama Eze, wanda ya fito daga yankin Mgbidi da ke karamar hukumar Oru ta yamma, bayan wani dan garin ya tsegunta wayan sanda.

A cewar Mba, mai laifin ya tabbatar da aikata laifin sannan kuma ya dauki yan sanda zuwa wajen da aka binne gawar marigayiyar.

Yace: “Baya ga fyade da Chukwuemeka Eze yayi wa baiwar Allah a karshen cin zarafin, yayi kokarin rufe laifin da ya aikata ta hanyar kashe ta.

“Amma kamar yadda muke yawan fada ma mutane babu laifi mai kyau a ko ina a fadin duniya.”

"Bayan aikata laifin, an tattaro cewa ya dauki wayar marigayiyar zuwa wani shago da niyan chajinsa.

“Wani dan Najeriya mai kula wanda ya kasance mallakin shagon ya kalli Chukwuemeka Eze wanda ya kawo wayan shagonsa sai ya lura daga hallayarsa cewa babu shakka wayar ba tasa bace,” Inji Mba.

Ya kara da cewa: “Jim kadan bayan ya juya bayansa, sai wannan mai shagon ya kunna wayar sannan kiran farko day a shigo daga yan uwar marigayiyar na jini ne wacce ta nemi Magana da yar uwarta.

KU KARANTA KUMA: Tsoho mai shekaru 68 ya yi wa ‘yarsa mai shekara 15 da kawayenta 2 fyade

“A wanna hirar ne ya gane cewa wayar ban a Eze bane.”

Har ila yau rundunar tace ta kama wasu masu laii da ke garkuwa da mutane, fashi da makami, da kuma mallakar kayayyaki ba bisa kaída ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel