Zan sake koma wa kujerar gwamnan jihar Bayelsa - Sylva

Zan sake koma wa kujerar gwamnan jihar Bayelsa - Sylva

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma babban jigo na jam'iyyar APC a jihar, Timipre Sylva, ya nemi matasan jihar da su shimfida goyon bayan a gare sa yayin da yake neman dawowa kujerar gwamnatin jihar a zaben watan Fabrairun 2020.

Sylva wanda ya rike akalar gwamnatin jihar Bayelsa a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2012, ya fayyace wannan kudiri yayin bikin murnar cikar sa shekaru 55 a duniya wanda aka gudanar a birnin Yenagoa na jihar.

Bayyanar kudirin tsohon gwamnan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da tsohon shugaban kungiyar sa ta yakin neman zabe kuma tsohon karamin ministan noma da raya karkara, Heineken Lokpobiri ya bayyana na sa kudirin a bisa goyon bayan Audu Ogbeh.

Audu Ogbeh wanda ya kasance tsohon ministan noma a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Asabar da ta gabata ya jaddada goyon baya a kan kudirin Lokpobiri na neman takarar kujerar gwamnatin jihar Bayelsa.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yayin da tsohon ministan noma ya aminta da cancantar Lokpobiri, a karshen makon jiya ya kuma kaddamar da ofishin yakin neman zaben sa a babbar hanyar Isaac Boro dake birnin Yenagoa na jihar Bayelsa.

KARANTA KUMA: Dalilin da yasa ya zama tilas Buhari ya gaggauta yiwa kujerarsa murabus - Tunde Adeleye

Kazalika jaridar ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Bayelsa mai ci, Seriake Dickson, ya yi gargadin cewa babu wanda zai ci gajiyar kujerar sa face dan takara da ya sanya Allah cikin al'amuransa tare da tsarkaka da dukkanin miyagun ababe na tsubbu ko neman kujerar mulki ta ko wane hali.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel