Magoya bayan Gwamna Bello sun ci zarafin 'yan jarida a Abuja

Magoya bayan Gwamna Bello sun ci zarafin 'yan jarida a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa magoya bayan Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi sun ci zarafin wasu manema labarai a hedkwatan jam'iyyar All Progressive Congress (APC) da ke babban birnin tarayya Abuja.

An gano cewa wasu magoya bayan gwamnan sun samu labarin cewa wasu na shirin yin zanga-zangar nuna kin amincewa da gwamnan ne kuma a yayin da suka iso hedkwatan jam'iyyar suka ga 'yan jaridan sai suka harzuka.

A cewar rahotanin da aka samu daga Abuja, shugaban APC na jihar Kogi, Abdullahi Bello ne ya jagoranci zanga-zangar da tayi sanadiyar yi wa wasu 'yan jaridar duka da kuma zarginsu da karbar cin hanci domin wallafa rahoto kan wadanda ke zanga-zangan kin amincewa da gwamnan.

DUBA WANNAN: An kama wasu mata 4 dumu-dumu suna madigo a Kwallejin Kimiyya a Kebbi

An kuma ce shugaban na APC ya yi barazanar kwace wayoyin salular wani dan jarida da ya ke zargin yana daukan hotuna a wurin amma sauran takwarorinsa ba su bari hakan ya faru ba.

A cewar The Punch, Mista Bello ya yi barazanar yi wa 'yan jaridar duka yayin da daya daga cikinsu ya ki mika wayar salularsa da shugaban na APC ya yi yunkurin kwacewa.

Jami'an tsaro da ke wurin ne su ka shiga tsakani domin kada rikicin ya kazanta.

Jim kadan bayan afkuwar hakan, wasu 'yan takarar gwamna a karkashin kungiyar Kogi State APC Governorship Aspirants Forum sunyi zanga-zanga a sakatariyar ta jam'iyyar APC na Abuja.

'Yan takarar sun nuna rashin jin dadin su kan rashin amfani da tsarin kato-bayan-kato wurin zaben dan takarar gwamna a jihar.

A cikin wasikar da mai magana da yawun kungiyar, Mohammed Ali ya aike wa shugaban jam'iyyar na kasa Adams Oshiomhole, ya ce, "Shirin da ake yi na amfani da tsarin amfani da wakilai wurin zaben 'yan takarar gwamna zai haifar da matsaloli da dama a ga jam'iyyar a jihar ta Kogi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel