Tsoho mai shekaru 68 ya yi wa ‘yarsa mai shekara 15 da kawayenta 2 fyade

Tsoho mai shekaru 68 ya yi wa ‘yarsa mai shekara 15 da kawayenta 2 fyade

Rahotanni sun kawo cewa rundunar yan sandan jihar Lagas ta damke wani tsoho mai shekara 68, wanda aka ambata da suna Isa Showunmi kan laifin yiwa yar cikinsa mai shekara 15 da wasu kawayenta biyu fyade.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Bala Elkana, ya bayyana wa manema labarai cewa, “yarinyar tasa ce ta kai rahoton lamarin ga yan sanda inda ta bayyana cewa mahaifin nasa ya dade yana lalata da ita cikin shekaru uku da suka gabata.

“Ta kara da cewa mahaifin nata ya kuma yi lalata da kawayenta biyu da suka ziyarceta a gidansu da ke Imota a yankin Ikorodu.

“Yarinyar ta ce, a baya bayan ma mahaifin nata ya yi mata fyade a ranar 23 ga watan Yuni, kuma ya amsa laifin sa a lokacin da ake bincikar sa kuma yazu hakama an gurfanar da shi a gaban kotu”.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Har yanzu ni cikakken dan jam'iyyar APC ne - Buba Galadima

Haka zalika, rundunar ‘yan sandan ta Legas ta kuma kame wani fasto mai suna Pope Paul da ake zargi laifin yi wa yarinya ‘yar shekaru 15 ciki ta kuma kame wani dattijo mai suna Aliyu Muhammad shi ma akan zargin yin lalata da ‘yar shekaru 14 a wani kango wadanda dukkan su a ka gabatar da su a kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel