Kotu ta bada umurni da a fallasa yan kwangila da suka lakume kudin gyaran lantarki

Kotu ta bada umurni da a fallasa yan kwangila da suka lakume kudin gyaran lantarki

-Kotu ta bada umurni da a fallasa yan kwangilar da suka karbi kudin gyaran wutar lantarki amma suka gudu da kudin ba tare da sunyi gayaran ba

-Hakan ya biyo bayan da kungiyar SERAP ta shigar da kara inda ta bukaci da a sanar da sunayen yan kwangilar da suka karbi kudin gyaran wutar lantarki tun dawowar dimukaradiyya a 1999

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake a jihar Legas ta bukaci gwamnatin tarayya da ta bayyana sunayen yan kwangila da suka ki yin gyaran wutar lantarki bayan kuma sun karbi kudin aikin.

Mataimakin daraktan kungiyar kare tattalin arzikin kasa da bin diddiki (SERAP) Kolawole Oluwade, ya bayyana cewa mai shari’a Chuka Obiazor ne ya bayar da umurnin a ranar juma’a 5 ga watan Yuli 2019.

Ya bayyana cewa alkalin ya bada umurnin a bayyana cikakken bayani akan yan kwangilan da aka baiwa kudin gyaran wutar lantarki tun dawowar dimukaradiyya a shekarar 1999.

A cikin watan Fabrairu ne SERAP ta kai tsohon ministan wutar lantarki, Babatunde Fashola kara kotu inda ta bukaci da a umurci Fashola ya bayyana sunayen yan kwangilar da aka ba aikin gyaran wutar lantarki da kuma inda yan kwangilan suke a yanzu, kamar yadda dokar yancin sanin bayanai ta bayar.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Sarkin Kano ne ya tunzura matan arewa suke kashe mazajensu - Hon. Zulyadaini Sidi Karaye

A cikin watan Mayu, ministan ya mikawa SERAP sunan wani dan kwangila guda daya, amma SERAP ta bayyana cewa tana bukatar sunayen sauran yan kwangilar da suka karbi kudin gyaran wutar amma suka lakume kudin.

A jawabin da SERAP ta fitar a ranar Lahadi 7 ga watan Yuli 2019, ta bayyana cewa alkalin ya umurci da “A bayyana cikakken bayani, a kuma yada sunayen kamfanonin da kuma inda yan kwangilan suke wadanda gwamnatoci suka ba kudi don gyaran wutar lantarki tun dawowar dimukaradiyya a 1999 amma suka gudu da kudin ba tare da sunyi aikin ba.”

Alkalin ya bayyana cewa “Kin bawa SERAP cikakken bayani akan kudaden da aka biya yan kwangila tun daga 1999 sabawa dokar yancin sanin bayanai ce ta 2011.”

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel