Ba kunya ba tsoron Allah: Tsohon gwamnan APC da matarsa sun kwashe motocin naira biliyan 1

Ba kunya ba tsoron Allah: Tsohon gwamnan APC da matarsa sun kwashe motocin naira biliyan 1

Asirin wani tsohon gwamnan APC na jahar Oyo, Abiola Ajimobi ya tonu, inda aka fallasa yadda tsohon gwamnan tare da matarsa da wasu manyan mukarrabansa suka yi awon gaba da motocin alfarma mallakin gwamnatin guda 26.

Binciken jaridar Premium Times ta bankado yadda Gwamna Abiola Ajimobi ya kwashe motoci guda 11 shi kadai da suka hada da Nissan Pathfinder, Lexus Jeep, Toyota Land cruiser guda 5, Lexus Jeep, Land cruiser SUV, da Toyota Hilux.

KU KARANTA: Zan farfado da duka matatun man Najeriya 4 kafin 2023 – Mele Kyari

Majiyar Legit.ng ta ruwaito uwargidar tsohon gwamnan kuwa ta samu motoci guda 6 da suka hada da Toyota Land cruiser SUV guda 2, Toyota Avensis, Hyundai guda 2 da kuma Renault Latitude.

Yayin da tsohon mataimakin gwamnan jahar ya yi awon gaba da motoci guda 4 da suka hada da Toyota Land Cruiser da Hilux guda 3, inda tsohon sakataren gwamnatin jahar Ishamel Alli ya tashi da motoci 2; Toyota Land cruiser da Prado SUV 2018.

Sauran wadanda suka ci gajiyar wannan watanda da tsohon gwamnan jahar Oyo ya yi sun hada da tsohon kaakakin majalisar dokokin jahar wanda ya samu Toyota land cruiser, da kuma tsohon shugaban ma’aikatan jahar daya samu motoci 2, Toyota Prado SUV da Toyota Hilux guda daya.

Majiyar ta tabbatar da cewa dukkanin motocin nan an sayesu ne tsakanin watan Janairu zuwa watan Feburairu na shekarar 2019, kuma mota mai karamin farashi a cikinsu ita ce ta naira miliyan 30, yayin da babbar ita ce ta naira miliyan 140.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel