Kotun zabe ta sanya rana don sauraren jawabin karshe a shari’ar Shehu Sani da Uba Sani

Kotun zabe ta sanya rana don sauraren jawabin karshe a shari’ar Shehu Sani da Uba Sani

-Kotun zabe ta Kaduna ta dage sauraron karar da Shehu Sani ya shigar zuwa 25 ga watan Yuli 2019 don sauraron jawabin karshe

-Shehu Sani na kalubalantar nasara Uba Sani ya samu a zaben sanata da ka gudanar a cikin watan Maris 2019

-Shehu Sani na bukatar kotun ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben

Kotun sauraron koken zabe dake a Kaduna ta dage zamanta zuwa ranar 25 ga watan Yuli 2019, don sauraron jawabin karshe daga bakin lauyoyi a shari’ar Shehu Sani da Uba Sani.

Sanata Shehu Sani na kalubalantar nasarar da Uba Sani ya samu a zaben sanata inda kuma ya bukaci kotun da ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Da yake zantawa da yan jarida a jiya Litinin 8 ga watan Yuli 2019 bayan zaman kotun, lauyan sanata Shehu Sani Morris A. Odeh (SAN) ya bayyana cewa an gama sauraron shaidu saboda sanata Uba Sani ya kasa gabatar da shaida ko guda.

Odeh ya bayyana cewa sanata Shehu Sani ya gabatar da shaidu guda biyu a lokacin da ake sauraron karar amma sanata Uba sani ya gaza gabatar da shaida ko guda daya.

KARANTA WANNAN: Miyagun da suka kashe hadimin gwamnan jahar Kogi sun fada komar Yansanda

Lauyan ya bayyana cewa “Abinda ake ciki yanzu shine, za mu dawo ranar 25 ga watan Yuli don mu gabatar da jawabin karshe, daga nan sai mu saurari hukunci.”

Ya kara da cewa “Abinda wadanda ake kara basu sani ba shine, karar da ake yi akan sabani tsakanin mutane daban take da kara kan aikata laifi. Wannan kara ce ta tsakanin mutane biyu, a saboda haka babu bukatar sai mun gabatar da shaida keke da keke kafin kotu ta karbe shi.”

Ya kara da cewa “Mun gabatar da shaidun mu, kuma komin karantarsu to ana tsammanin su karyata su, amma suka gaza yin hakan.”

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel