Alkalai sun gaza tsaida hukunci a kan hallacin takarar Shugaba Buhari a zaben 2019

Alkalai sun gaza tsaida hukunci a kan hallacin takarar Shugaba Buhari a zaben 2019

Babban kotun daukaka kara da ke cikin Garin Abuja ya yi wani zama a game da shari’ar da a ke yi kan takarar shugaban kasa Buhari a zaben 2019, inda a ke zargin cewa bai da isassun takardu.

Alkalai uku a karkashin jagorancin babban Mai shari’a Atinuke Akomolafe-Wilson, su ka zauna a jiya Litinin, 8 ga Watan Yuni, 2019. Alkalan ba su fitar da wani tsayayyen mataki ba tukuna.

Alkali mai shari’a Atinuke Akomolafe-Wilson, ya bayyana cewa kotu za ta bayyana hukuncin da ta dauka nan gaba kadan. Sai dai babban Mai shari’ar bai bayyana lokacin da za su zauna din ba.

Lauyan wanda ya shigar da kara a gaban kotu watau Ukpai Ukairo, ya hakikance a kan cewa shugaba Buhari bai da ilmin da a ke bukata kafin a tsaya takarar shugaban kasa a zaben Najeriya.

KU KARANTA: Yadda a ka mikawa INEC takardun zaben karya a 2019 – Shaidan PDP

Babban Lauyan ya sanar da kotu cewa Buhari bai gabatar da satifiket dinsa a cikin fam din takarar da ya mikawa hukumar zabe INEC ba. Lauyan ya nuna cewa wannan ya sabawa doka.

Mai karar ya na so kotu ta ruguza takarar shugaba Buhari a dalilin rashin satifiket. Lauyan ya na karar cewa Buhari bai mallaki ko da mafi karancin ilmin da a ke bukata wajen yin takara ba.

Lauyoyin da ke kare shugaba Muhammadu Buhari sun nemi Alkalan kotun su yi watsi da wannan kara. Tuni Lauya Abdullahi Abubakar ya fadawa kotu cewa lokacin sauraron karar ya wuce.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel