Wata sabuwa: Har yanzu ni cikakken dan jam'iyyar APC ne - Buba Galadima

Wata sabuwa: Har yanzu ni cikakken dan jam'iyyar APC ne - Buba Galadima

- Buba Galadima ya bayyana cewa har yanzu shi cikakken dan jam'iyyar APC mai mulki ne

- Ya fadi hakan ne akan hujjar da ya bayar ta cewa yana daya daga cikin mutane tara da suka kafa jam'iyyar

- Bayan haka ya bayyana cewa ya goyi bayan babbar jam'iyyar adawa ne saboda suna da abu iri daya

A wata hira da BBC ta yi da fitaccen dan adawar nan na jam'iyyar APC, wanda kuma yake daya daga cikin wadanda suka samar da jam'iyyar, Alhaji Buba Galadima, ya bayyanawa BBC cewa har gobe shi cikakken dan jam'iyyar APC ne.

Ya bayar da dalilin cewa yana daya daga cikin mutane tara da suka kafa jam'iyyar APC a kasar nan.

Ga yadda hirar ta su ta kasance:

Mene ne gaskiyar ikirarin da ka yi na cewa kai dan jam'iyyar APC ne?

Ni da gidanmu? ni fa na kafa gidan. Ni na ajiye tubalin gina wannan jam'iyya. Ina daya daga cikin mutum tara da suka hannu aka yi wannan jam'iyya.

Haka kawai sai in gudu in bar ladana? Wa zan bar wa? Duk ranar dana ga dama zan fita, amma a yau da na ke magana da kai, ni dan jam'iyyar APC ne cikakke.

Yanzu haka kawai ni na zo na gina gidana, kawai sai wani agola yazo yace zai kore ni? Ai sai inda karfina ya kare. Dalilin da yasa har yanzu basu isa su zo su kalubalance ni ba, ko kuma suce sun kore ni, in kuma sun isa ga fili ga mai doki.

KU KARANTA: Allah wadan naka ya lalace: Wani mutumi ya shekara biyu yana zina da 'yar cikinsa, yayin da yake sanyata ta zubar da ciki idan ya shiga

Amma mai yasa kayi jam'iyyar PDP a zaben 2019?

Don mun yi hadaka ne da jam'iyyar PDP na tabbatar da mun fito da muzahiri cikakken mutum wanda ya san abin da yake yi, wanda yake da ilimi da zai iya ciyar da kasar nan gaba. Wanda zai kawo zaman lafiya a kasa, wanda kuma zai ciyar da kasar nan gaba ta hanyar habaka tattalin arzikin kasa.

Ai mun samu yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin kungiyarmu ta jam'iyyar APC da muke kalubalantar APC tana tafiyar guragu da kuma mu.

Kaje kotun zabe ka bayar da shaida ranar Alhamis, me ka ce?

Na farko dai babbar shaida ta ita ce nuna wa duniya cewar Muhammadu Buhari bai cancanci ya tsaya shugabancin Najeriya ba, saboda bashi da cikakken ilimi bisa doka, da zai ba shi damar tsayawwa wannan zaben.

Na biyu, alkaluman da muke da shi a lokacin da aka yi zabe ya nuna cewa Atiku Abubakar shine wanda ya lashe wannan zaben.

Mun gabatar da takardu na shaida wanda ya nuna hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel