Rundunar sojin ruwa tayi kamen buhunna 825 na haramtattun kaya

Rundunar sojin ruwa tayi kamen buhunna 825 na haramtattun kaya

-Runndar sojin ruwa ta Najeriya ta yi nasarar damke buhunna 825 na shinkafa da aka shigo da su a boye

-Shugaban makarantar lafiya ta sojin ruwa dake a Offa, jihar Ilorin Ayodele Ogunniyi ne ya bayyana haka

-Ayodele ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin a cikin motoci 15 ko wacce dauke da buhunna 55

Runndar sojin ruwa ta Najeriya a Offa dake a jihar Kwara ta yi nasarar damke buhunna 825 na shinkafa da aka shigo da su a boye daga jihar Oyo.

Da yake zantawa da manaima labarai a lokacin da ake nuna wadanda aka kama da kayan nasu, kwamanda na makarantar lafiya ta sojin ruwa dake a Offa, keftin Ayodele Ogunniyi, ya bayyana cewa an yi kamen ne da misalin karfe 5:00 na safiyar ranar Litinin 8 ga watan Yuli 2019.

Ayodele ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin a cikin motoci 15 ko wacce dauke da buhunna 55 na shinkafar kasar waje wanda idan aka hada jumlarsu zai kama 825.

Da yake zantawa da yan jarida, daya daga cikin wadanda aka kama, wanda kuma direban daya daga cikin motocin ne, Ahmad Mustapha ya bayyana cewa sun zo daga Shaki dauke da kayan don a siyar da su a Offa, jihar Kwara.

Mustapha ya bayyana cewa kayan ba nashi bane inda ya bayyana cewa wani mutum ne da ake kira da ‘Pilot’ mazaunin Shaki ya aike su don su kai kayan.

KARANTA WANNAN: Miyagun da suka kashe hadimin gwamnan jahar Kogi sun fada komar Yansanda

A ranar 8 ga watan Afirilu 2019, Legit.ng ta ruwaito cewa kungiyar masu sarrafa shinkafa ta Najeriya, ta bayyana cewa an shigo da fiye da buhunna miliyan 20 na shinkafa daga kasar waje a tsakanin watan Janairu zuwa watan Maris na wannan shekarar.

Shugaban kungiyar, Mohammed Abubakar ya yi kira ga gwamnati da ta tsaurara matakai don magance matsalar safarar shinkafa saboda hakan na dakile shirin gwamnati na bunkasa samar da shinkfar gida.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel