‘Yan Sanda sun ce Sulhun da a ke yi ya jawo raguwar hare-hare a Zamfara

‘Yan Sanda sun ce Sulhun da a ke yi ya jawo raguwar hare-hare a Zamfara

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Zamfara, Usman Nagogo, ya bayyana cewa irin ta’adin da a ke yi a jihar ya ragu da kusan 98% a halin yanzu. An samu hakan ne saboda sulhun da a ke shirin yi.

A Ranar Litinin, 8 ga Watan Yuni, 2019, Usman Nagogo ya ke cewa yarjejeniyar sulhu da zaman lafiya da a ka fara yi a jihar Zamfara ya taimaka wajen rage hare-haren da a ka saba fuskanta.

Babban jami’in ‘yan sandan na jihar Zamfara ya nuna cewa su na samun nasara wajen sha’anin tsaron. Nagogo ya ke cewa sun yi zama daban-daban da Hausawa da Fulani da kuma ‘Yan banga.

A cewar Kwamishinan, bayan wadannan mabanbantan zama da a ka yi da bangarorin, za a kira wani taro da dukkaninsu domin tabbatar da dakatar da buda wuta da a ke yi a jihar na Zamfara.

KU KARANTA: Ndigbo, SERAP, da PDP su na so Buhari ya canza Hafsun Sojoji

“A karshen zaman da mu ka yi, an yi ta zargin juna, amma mun samu fahimta, wanda a sanadiyar haka a ka saki mutum 50 da a ka yi garkuwa da su a hannun ‘yan sa kai da masu satar jama’a."

Idan ba ku manta ba, sabon gwamna Bello Matawalle ya shiga wata yarjejeniyar zaman lafiya kwanan nan a karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sandan jihar na Zamfara Usman Nagogo.

Har wa yau Nagogo ya nuna cewa za su fara karbe makamai daga hannun tubabbun tsagerun da ke jihar domin a wanzar da zaman lafiya kamar yadda yajejeniyar sulhun da a ka tsara ya tanada.

Nagogo ya ce: “A halin yanzu Fulani su na shiga kasuwanni salin-alin ba tare da an kashe kowa ko a yi wa wani kwarzane ba. Hakan na nuna cewa an ci ma manufar sulhu da zaman lafiya.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel