Miyagun da suka kashe hadimin gwamnan jahar Kogi sun fada komar Yansanda

Miyagun da suka kashe hadimin gwamnan jahar Kogi sun fada komar Yansanda

Rundunar Yansandan jahar Kogi ta sanar da kama miyagun da take zargi da hannu cikin kashe hadimin gwamnan jahar, Yahaya Bello, mai suna Yusuf Adabenege Onivehu, kamar yadda rahoton Daily Trust ya bayyana.

Kwamishinan Yansandan jahar, Hakeem Busari ne ya bayyana haka yayin da yake bayyana mutanen ga manema labaru a garin Okene, a ranar Litinin, 9 ga watan Yuli, inda yace sun samu nasarar kama mutanen ne ta hanyar aikin hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.

KU KARANTA: Saurayi ya hada baki da budurwarsa sun sace mahaifinta don neman kudin bikin aurensu

Kwamishina Busari ya bayyana sunayen miyagun kamar haka; Yusuf Abdulmumeen, Abona Jafar, Yusuf Tijani, Yusuf Abdulkarim, Yusuf Kebiru da Yusuf Lawal, kuma dukkaninsu sun tabbatar da hannu cikin kashe marigayi Yusuf.

Haka zalika miyagun sun bayyana cewa suna gudanar da aikin fashin makami da kuma garkuwa da mutane a tsakanin jahohin Edo, Osun da kuma jahar Kogi, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaitosu suna fadi.

Daga cikin abubuwan da Yansanda suka kwato daga wajensu akwai bindiga kirar AK 47 guda biyu, bindigar Pump Action, alburusai 100 da sauran makamamai.

Da yake nasa jawabin, Gwamna Yahaya Bello wanda ya halarci taron bayyana miyagun ga manema labaru ya gargadi duk masu aikata miyagun laifuka a jahar Kogi dasu daina ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Gwamna Bello yace a shirye ya kashe kudin jahar Kogi gaba daya wajen tsaron al’ummarta, tare da kare dukiyoyinsu da kuma rayukansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel