Saurayi ya hada baki da budurwarsa sun sace mahaifinta don neman kudin bikin aurensu

Saurayi ya hada baki da budurwarsa sun sace mahaifinta don neman kudin bikin aurensu

Tabdijam! Wani saurayi mai suna Emmanuel Sunday ya hada baki budurwarsa, Chinaza Nwogu suka yi garkuwa da mahaifinta mai shekaru 88 a duniya, Pa Njoku-Louis, wai don su samu kudin fansa da zasu gudanar da bikin aurensu dashi.

Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan Najeriya, DCP Frank Mba ne ya bayyana haka yayin da yake bayyana mutanen ga manema labaru, inda yace Sunday dan shekara 29 ya hada baki da Chinaza yar shekara 19 da kuma dan uwanta wajen sace surukinsa.

KU KARANTA: Babban Faston Najeriya ya yi kira ga Buhari ya yi murabus daga kujerar shugaban kasa

Kaakakin yace manufar mutanen uku na yin garkuwa da wannan tsoho shine domin iyalansa su biyasu kudin fansa, ta yadda zasu samu isashshen kudi da zasu gudanar da bikin aurensu dasu sakamakon Chinaza tana dauke da ciki wata 8, ka ga sai a sha shagali iya shagali.

Sai dai kaakakin yace yayan Chinaza wanda shine ya fara kawo shawarar sace mahaifinsa ga saurayin kanwarsa ya cika wandonsa da iska, amma har yanzu suna bin sawunsa domin farautoshi cikin dan lokaci.

Kafin su kai ga sace dattijon, mutanen uku sun sace motarsa kirar Sienna, wanda suka bada jinginarta suka amshi bashin N40,000 daga hannun wani mutumi Emeka Ejike dake unguwar Nekede a garin Owerri, haka zalika sun taba sace yarinyar yar shekara 5 Dobrah Chidinma, basu saketa ba sai da aka biyasu naira miliyan 1.2

Da yake jawabi ga manema labaru, Sunday Emmanuel ya tabbatar da aikata laifin, inda yace abokinsa, kuma yayan budurwarsa ne ya kawo shawarar yin garkuwa da mahaifinsu domin su samu kudin yin bikin aurensa da kanwarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel