Don dole na sa hannu a takardun INEC saboda gudun a kore ni daga N-Power – Wakilin PDP

Don dole na sa hannu a takardun INEC saboda gudun a kore ni daga N-Power – Wakilin PDP

Mun samu labari cewa Mohammed Tata, wani shaida da jam’iyyar PDP ta gabatar a gaban kotu, ya bayyana yadda a ka matsa masa lamba wajen sa-hannu a kan takardun zaben shugaban kasa.

A Ranar Litinin, 8 ga Watan Yuni, 2019, Mohammed Tata, ya fadawa kotu cewa dole ta sa ya rattaba hannu a kan takardun zaben bayan an yi barazanar cire sunansa daga cikin Ma’aikatan N-Power.

Tata ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke amsa tambaya daga bakin wani Lauyan hukumar zabe na kasa na INEC mai suna Yunus Usman. Wakilin na PDP a zaben na 2019, ya ce magudi a ka yi a zaben.

“Baraza a ka rika yi mani domin in sa hannu a kan takardun zaben a cikin matsi. An fada mani cewa za a goge suna daga cikin masu amfana da tsarin N-Power muddin na ki sa hannu na.”

KU KARANTA: Kotun zabe: Wani shaidan Atiku ya cirewa INEC zani a kasuwa

A game da kuri’u fiye da 700 da Buhari da APC su ka samu a akwatin sa, sai ya ce:

“Babu kuri’u domin kuwa ba a yi zabe ba. Ni Musulmi ne, na san hukuncin kaddara. Ko da PDP ko APC ta ci zabe, ba zab damu ba. Amma abin da na ke so shi ne a yi adalci a Najeriya.”

Wannan Bawan Allah ya ke cewa nasarar PDP ko APC ba za ta dada sa da kasa ba, amma ya tabbatar da cewa babu shakka ba ayi zabe a yankinsa ba domin kuri’un karya a ka gabatarwa INEC.

Malam Tata ya kuma sanar da kotu cewa: “Babu wanda ya bani takardun sakamakon zaben, domin ba a samu natsuwar da za ayi zabe ba.”

Tata wanda shi ne shaida na biyar da Atiku Abubakar ya gabatar, ya ce ya fadawa hukuma yadda a ka yi magudi amma ba a dauki matakin komai ba. Sai dai ya ce har yanzu yana aikinsa na N-Power.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel