Dalilin da yasa ya zama tilas Buhari ya gaggauta yiwa kujerarsa murabus - Tunde Adeleye

Dalilin da yasa ya zama tilas Buhari ya gaggauta yiwa kujerarsa murabus - Tunde Adeleye

Shehin malamin addinin kirista kuma babban limamin Cocin Eccelesiastical dake yakin Neja Delta, Rabaran Tunde Adeleye, ya kirayi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta sauka daga kujerar sa.

Babban limamin ya ce gwamnatin shugaban kasa Buhari ta gaza samun goyon bayan mafi rinjayen kaso na al'ummar kasar nan. Ya ce mafi kusancin hadiman shugaba Buhari sun kasance mayaudara da a halin yanzu sun kai shi kuma sun baro.

Ya ce a sanadiyar gurguwar shawara da rashin fadin gaskiya na miyagun hadimai da kuma munanan mashawarta, ya sanya gwamnatin shugaban kasa Buhari ta gaza fidda kasar nan zuwa tudun tsira illa iyaka jefa ta cikin halin ni 'ya su.

Rabaran Tunde yayin gabatar da hudubar sa a babban cocin Cathedral of the Holy Trinity dake birnin Calabar na jihar Cross River, ya yi tsokaci a kan halin da kasar nan ta ke ciki a yanzu.

KARANTA KUMA: Obasanjo ne mafarar duk wata matsala a Najeriya - Sarkin Legas

Ya jaddada cewa dole ne hadin kai ya tabbata a kasar nan, kuma bugu da kari sauya tsarin kasa tare da yi mata garambawul ya zamto ka-in-da-la-in wajen fidda kasar nan zuwa tudun mun tsira.

A watan Afrilun 2017, Shehin malamin addinin kirista kuma babban limamin Canterbury, Justin Welby, ya ziyarci Buhari a 'yar karamar fadar shugaban kasar Najeriya dake birnin Landan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel