Mambobin PDP a majalisar wakilai sun caccaki 
jam'iyyar akan dakatar da Elumelu

Mambobin PDP a majalisar wakilai sun caccaki jam'iyyar akan dakatar da Elumelu

Wasu mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar wakilai sun caccaki jam’iyyar kan dakatar da Ndudi Elumelu, Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai.

Da suke jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli, yan majalisar sunce an zabi Elumelu da sauran jami’an marasa rinjaye a majalisar ne bisa ka’ida.

Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai, ya sanar da Elumelu a matsayin Shugaban marasa rinjaye, Toby Okechukwu a matsayin mataimakin Shugaban marasa rinjaye, Gideon Gwani a matsayin bulaliyar marasa rinjaye daa kuma Adesegun Adekoya a matsayin mataimakin bulaliyar marasa rinjaye.

Kakakin majalisar yace an sanar masa da zabansu a wata wasika daga bangaren marasa rinjaye.

Amma PDP, wacce ta mara wa yan takara daban baya ciki harda Kingsley Chinda a matsayin Shugaban karasa rinjaye tayi adawa da yunkurin sannan ta dakatar da Elumelu da sauran da Gbajabiamila ya sanar.

Da suke jawabi ga manema labarai a Abuja, yan majalisar marasa rinjaye sun yi kira ga PDP da ta dage dakatarwar sannan ta nemi sulhu a maimakon haka.

KU KARANTA KUMA: Kotu zaben Shugaban kasa: Ba ayi zabe ba a rumfata, sun rubuta sakamako ne - Shaida

Ochiglegor Idagbo daga jihar Cross River, wanda yayi Magana a madadin sauran, yace yayinda yan majalisar ke ci gaba da biyayya ga PDP, dakatar da zababbun jami’an zai dada tabarbarar da lamarin ne.

“Idan har anyi laifi a wannan tsarin, kamata yayi masu laifin su kasance dukkaninmu mu 111 da muka zabi takwarorinmu domin su jagorance mu, ba wai dakatar da mambobi bakwai na jam’iyyarmu mai girma ba,” inji shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel