Ba gaskiya bane rade-radin cewa jami’in Kwastam ya nemi yiwa shugaban Hukumar juyin mulki – Inji Kwastam

Ba gaskiya bane rade-radin cewa jami’in Kwastam ya nemi yiwa shugaban Hukumar juyin mulki – Inji Kwastam

Hukumar kwastam ta karyata labarin da ke yawo k cewa wai wani jami’inta mai suna Nura Dahiru, ya nemi ya haye kujerar shugaban hukumar a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli a birnin tarayya, Abuja.

Kakakin rundunar Joseph Attah ya bayyana cewa Nura ya garzayo hedikwatar hukumar a safiyar Litinin sanye da kaya dauke da mukamin mataimakin shugaban hukumar Kwastam, Wato DCG.

Attah ya ce ko da suka tambaye shi ko me ya sa ya saka wadannan kaya da rataye da mukamin DCG sai ya fara sumbatu, da suka kauce wa hanya. Daga nan ne suka gane cewa lallai wannan jami’i bashi da lafiya ne.

"Da muka gano haka sai muka garzaya da shi asibiti domin a duba shi."

A karshe Attah ya roki mutane da su taya jami’in da addu’a sannan ayi watsi da karerayin da ame yadawa wai ya nemi ya dare kujerar shufaban hukumar ne, Hameed Ali.

KU KARANTA KUMA: Kotu zaben Shugaban kasa: Ba ayi zabe ba a rumfata, sun rubuta sakamako ne - Shaida

Da farko dai mun ji cewa wani jami'i mai matsayin mataimakin supritandan ASC mai suna, Nura Dalhatu, ya karawa kansa girma zuwa matsayin DCG kuma yayi ikirarin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bashi umurnin kwace ragamar mulki daga hannun Kanal Hamid Ali.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel