Buhari ya nada Malam Balarabe a matsayin jagoran shirin FADAMA III

Buhari ya nada Malam Balarabe a matsayin jagoran shirin FADAMA III

Gwamnatin tarayya ta amince da nadin Malam Abdulrasaq Balarabe a matsayin sabon jagoran shirin FADAMA III AF na kasa.

Mista Bashir Dayyabu, jami'in sadar wa na kasa a ofishin shirin Fadama, ne ya sanar da hakan a wani jawabi da ya fitar a Abuja ranar Litinin.

Dayyabu ya ce sanarwar nadin Malam Balarabe na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin babban sakataren ma'aikatar noma da raya karkara.

A cewar sanarwar, Balarabe ya kammala karatun digiri na farko a bangaren ilimin noma a jami'ar Usman Danfodiyo a shekarar 19991, sannan ya na da digiri na biyu a bangaren tsimi da harkar noma (Agricultural Economics)

Ya fara aiki a matsayin jami'in harkar noma a ma'aikatar noma a shekarar 1993 kafin daga bisani ya koma bangaren kula da shirye-shirye na musamman a bangaren noma a shekarar 1996 a matsayin jami'i mai tabbatar tasirin shirye-shiryen.

DUBA WANNAN: Rumbun tattara sakamakon zabe: Shaidar Atiku 'ya kwance wa INEC zani a gaban kotu'

Daga bisani Balarabe ya koma ma'aikatar noma da albarkatun ruwa ta tarayya inda ya kai mukamin mataimakin jagoran aiyuka na musamman.

Balarabe na da gogewa ta tsawon shekara 20 a bangaren harkokin noma da suka hada da tsare-tsare, sa ido, tantancewa da bayar da shawarwari.

Ya haalrci tarukan karin ilimi da horo a bangaren harkokin noma a gida da ketare.

A cewar sanarwar, tuni Balarabe ya fara aiki a sabon mukamin da aka nada shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel