Kotu zaben Shugaban kasa: Ba ayi zabe ba a rumfata, sun rubuta sakamako ne - Shaida

Kotu zaben Shugaban kasa: Ba ayi zabe ba a rumfata, sun rubuta sakamako ne - Shaida

Wakilin rumfar zabe na Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayi zargin cewa ba a gudanar da zabe ba a rumfar zabensa yayin zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Febrairu.

Mohammed Usman Tata, wanda ya bada shaidan a gaban kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa a ranar Litinin, yace an razana wakilai a rumfar zabensa sannan aka tursasa su sanya hannu a takardun sakamakon zabe ko kuma su rasa matsayinsu a shirin NPower.

Tata, wanda rumfar zabensa ya kasance a karamar hukumar Gwaram dake jihar Jigawa, ya kai rahoton lamarin zuwa ga jam’iyyar PDP, sannan kuma ya kai rahoto zuwa ga hukumar INEC amma kuma ba a dauki mataki ba.

Lauyan INEC, Yunus Ustaz Usman (SAN) ya bukaci sanin ko yana korafi ne saboda an doke jam’iyyarsa a zaben, sai yace yana da sha’awar ganin anyi adalci ne a Najeriya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Mista Peter Uzioma Obi, shaida na biyu da jam'iyyar PDP da dan takarar ta a zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar, suka gabatar a gaban kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa, ya ce kuskure ne hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta ce ba ta da rumbun tattara sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu.

Obi ya bayyana hakan ne yayin da aka kira shi a gaban kotun a matsayin shaida a karar kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da INEC ta bayyana shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da jam'iyyar APC a matsayin wadanda suka yi nasara.

KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwa 9 da sabon Shugaban NNPC yayi alkawarin yi

Obi, wanda ya bayyana cewa ya yi aikin zabe a matsayin RATECH (Registration Area Technician) a jihar Ribas lokacin zabukan shekarar 2019, ya bayyana cewa INEC ta basu horo a kan yadda zasu aika mata sakamakon zabe zuwa babban rumbunsu na tattara sakamako.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel