Muhimman abubuwa 9 da sabon Shugaban NNPC yayi alkawarin yi

Muhimman abubuwa 9 da sabon Shugaban NNPC yayi alkawarin yi

Mallam Mele Kolo Kyari a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli ya kama aiki a matsayin manajan darakta na kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) na 19 bayan anyi bikin mika ragamar mulki a Abuja.

Yayinda ya karbi shugabancin kamfanin Mallam Kyari ya dauki alkawara da dama ciki harda gudanar da abubuwa a bayyane domin amfanin yan Najeriya.

Mallam Kyari ya dau alkawarin yin wadannan abubuwan:

1. Ba za mu taba yin kuskure da gan-gan ba.

2. Gare ku ýaýana, kada ku karbi kyaututtuka daga hannun kowa; ba nawa bane.

3. Ga kamfaonin main a kasa da kasa (IOCs), za mu yi aiki tare da ku, zai kasance nasara a koda yaushe.

4. Za mu mayar da hankali akan tsammanin yan Najeriya- za a samar da fetur, gas da sauran kayayyaki.

5. Za mu mayar da wannan kamfani na duniya ta hanyar aiwatar da ayyuka mafi inganci a duniya.

6. Ba za mu iya bayyana kowani bayani ba.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya dawo Abuja bayan taron AU

7. Za mu samar da ma’aikatu hudu kafin Buhari ya bar mulki a 2023.

8. Zuwa lokacin da Baba (shugaba Buhari) zai bar mu;lki, ya zama dole kasar nan ta zama cikakkiyar mai fitar da kayayyakin fetur.

9. Shirinmu shine habbaka danyen mai daga gangar mai miliyan 3 kowace rana zuwa gangar mai biliyan 40 zuwa 2023.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel