Obasanjo ne mafarar duk wata matsala a Najeriya - Sarkin Legas

Obasanjo ne mafarar duk wata matsala a Najeriya - Sarkin Legas

Sarkin Legas Mai martaba Oba Rilwan Akiolu, ya ce tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo, ya kasance babban ginshiki kuma tubalin duk wata matsala a kasar nan.

Mai martaba Akiolu ya bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da wani sabon littafi da wani jigon APC, Cif Olusegun Osoba ya wallafa a kan kasadar dake cikin siyasa da kuma aikin jarida.

Babban taron da aka gudanar a Otol din Eko dake unguwar Victoria Island ta jihar Legas, ya samu halarcin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan, mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ibrahim Wase.

Saura jiga-jigan da suka halarci taron sun hadar da; kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar APC, Bola Tinubu, gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson, tsaffin gwamnoni, ministoci, sarakunan gargajiya da kuma wasu gwamnonin yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Sarki Akiolu yayin kafa shaida da wasu jimloli da Cif Osoba ya wallafa a sabon littafin sa, ya yi ikirarin cewa a baya tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yaudari gwamnonin jam'iyyar AD, Alliance for Democracy da kuma kungiyar Yarbawa ta Afenifere.

Cikin kalaman sa ya ce "matsalar da muke fama da ita a kasar nan ita ce kuma ba zan daina fadin hakan ba, tabbas babbar matsalar Najeriya lamba daya ba a halin yanzu ita ce Obasanjo".

KARANTA KUMA: Buba Galadima ya fadi dalilin sa na juyawa Buhari baya

Yayin da tabbatar da Obasanjo a matsayin madubi na yaudara, kazalika ya buga misali da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, inda ya ce shi ganau ne ba jiyau ba.

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya gargadi tsohon shugaban kasa Obasanjo a kan kada ya kuskura adawar sa da Buhari ta mayar da shi dattijon wofi.

Martanin tsohon gwamnan na zuwa ne yayin da Obasanjo ya yi furucin cewa ta'addancin masu garkuwa da mutane da kuma mayakan Boko Haram na ci gaba da aukuwa da manufar gwamnatin Buhari ta assassa akidar addinin musulunci a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel