Karfin hali ko ganganci: Wani hafsan kwastam ya yi kokarin yiwa Hameed Ali juyin mulki

Karfin hali ko ganganci: Wani hafsan kwastam ya yi kokarin yiwa Hameed Ali juyin mulki

- Wani matashin hafsan hukumar kwastam ya shiga ofishin Hameed Ali da niyyar kwace mulki

- An kaishi asibiti domin an lura akwai alamun tabin hankali tattare da shi

A ranar Litinin ne wani jami'in hukumar hana fasa kwabri mai matsayin mataimakin supritandan ASC mai suna, Nura Dalhatu, ya karawa kansa girma zuwa matsayin DCG kuma yayi ikirarin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bashi umurnin kwace ragamar mulki daga hannun Kanal Hamid Ali.

Masu idanuwan shaida a hedkwatan hukumar dake Abuja sun bayyanawa jaridar The Cable cewa ya shigo ofishin da safiyar Litinin sanye da kayan sarki mai dauke da tambarin babban hafsa, kuma ya shiga ofishin kwantrola janar, Hameed Ali.

Karfin hali ko ganganci: Wani hafsan kwastam ya yi kokarin yiwa Hameed Ali juyin mulki

Nura Dalhatu
Source: Facebook

KU KARANTA: Duk da bidiyon da ya bayyana karara, Sanata Abbo ya karyata dukan matar aure, kotu ta bashi beli

Daya daga cikin majiyoyin yace: "Yayinda ya shigo, hafsoshi suka fara sara masa saboda yana dauke da tambarin babban hafsa."

"A watan Mayu, ya daura a shafin Facebook cewa shugaban kasa ya umurcesa ya karbe ragamar mulki daga hannun Hameed Ali, kuma yau da muka ganshi da sabuwar matsayi, mun dauka da gaske ne an kara masa matsayi kuma da gaskene Buhari umurcesa."

Ya shiga ofishin kwantrola Janar, ya zauna a zauren ofishin yana jiran kwantrola janar ya mika masa ragama."

Kakakin hukumar kwastam, Joseph Attah, ya alanta cewa an garzaya da Nura Dalhatu asibiti bayan an lura cewa yanada tabin hankali.

Yace: "Ya bayyana karara cewa ba cikin isasshen lafiya yake ba."

Ya ce an kaishi asibiti domin dubasa da kulawa da shi kuma yana bukatar yan Najeriya su taimaka masa da addu'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel