Gwamna Badaru Talamiz ya halaraci gangamin wa’azin kasa na Izala

Gwamna Badaru Talamiz ya halaraci gangamin wa’azin kasa na Izala

Gwamnan jahar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar Talamiz ya samu halartar gangamin wa'azin kasa wanda kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'a wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta shirya a garin Hadejia, Jihar Jigawa.

Gwamnan ya halarci gangamin ne daya gudana a filin fadar Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Abubakar Adamu Maje, a ƙarƙashin jagorancin shugaban Izala ta kasa, Sheikh Bala Lau.

Gwamna Badaru Talamiz ya halaraci gangamin wa’azin kasa na Izala

Gwamna Badaru Talamiz ya halaraci gangamin wa’azin kasa na Izala
Source: Facebook

KU KARANTA: Allah Ya tona asirin matashin daya shahara wajen satar wayoyin salula a Masallatai

Haka zalika taron ya samu halartar manyan malamai daga ciki da wajen ƙasar nan, tare da dubun dubatan al’umma Musulmai da suka yi tururuwa domin sauraron nasihohi daga bakin Maluma.

Gwamna Badaru Talamiz ya halaraci gangamin wa’azin kasa na Izala

Gwamna Badaru Talamiz ya halaraci gangamin wa’azin kasa na Izala
Source: Facebook

Da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Badaru ya yi wa manyan malamai da sauran mahalarta taron maraba da zuwa jahar Jigawa domin gudanar da wannan muhimmin lamari.

Bugu da kari gwamnan ya yi musu alƙawarin samar ma kungiyar Izala katafaren filin da zasu gina jami'ar musulunci a garin na Hadejia, daga karshe gwamnan ya yi kira ga malamai da su cigaba da yi wa ƙasar nan addu'ar samun cigaba, zaman lafiya da yalwar arziƙi.

Gwamna Badaru Talamiz ya halaraci gangamin wa’azin kasa na Izala

Gwamna Badaru Talamiz ya halaraci gangamin wa’azin kasa na Izala
Source: Facebook

A hannu guda kuma, gwamnan jahar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana jama’an Arewa a matsayin mutanen da suka fi inganci da rikon amana fiye da sauran yankunan Najeriya, amma kuma yankin Arewacin kasar itace koma baya a wajen cigaba.

El-Rufai ya bayyana haka ne a yayin wani taro da kungiyar Northern Hibiscus ta shirya a garin Kaduna a karshen makon data gabata, inda yace akwai bukatar matasan Arewa su tashi tsaye don kawo cigaba a yankin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel