Da duminsa: Duk da bidiyon da ya bayyana karara, Sanata Abbo ya karyata dukan matar aure, kotu ta bashi beli

Da duminsa: Duk da bidiyon da ya bayyana karara, Sanata Abbo ya karyata dukan matar aure, kotu ta bashi beli

Duk da bidiyon na'urar CCTV da bazu a duniya da na afuwar da ya nema, Sanata Elisha Abbo ya musanta zargin da ake masa na marin wata matar aure, Bibra, a shagon siyar da kayan jima'i dake birnin tarayya Abuja.

Elisha Abbo ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayinda hukumar yan sanda ta gurfanar da shi a kotun majistare dake unguwar Zuba, babbar birnin tarayya Abuja.

Alkalin majistaren ya bashi belin milyan biyar bayan an tuhumeshi da aikata laifuka biyu na cin zarafi.

Alkalin ya kara da cewa daga cikin sharrudan beli sai Sanatan ya gabatar da mutane biyu da zasu tsaya masa domin tabbatar da cewa ya halarci zaman kotu a lokacin da ake bukatansa.

Mun kawo muku a baya cewa Hukumar yan sandan Najeriya hallaro da Sanata Elisha Abbo kotun Majistare dake unguwar Zuba, Abuja domin gurfanar da shi kan laifin cin zarafi.

An tattaro cewa masu gudanar da bincike sun tabbatar da cewa lallai hujjan da aka gabatar kan sanatan jam'iyyar PDP, Elisha Abbo, mai wakiltar Adamawa ta Arewa inda yake ya waskawa wata matar aure mari gaskiya ne.

Hakazalika Sanata Abbo ya amsa wannan laifin a jawabin da ya gabatar a hedkwatan jam'iyyar PDP a makon da ya gabata inda ya nemi gafarar matar, matan Najeriya, da kuma yan kasa ga baki daya.

Wannan kadai ya isa ya zama hujja akansa a gaban kotu.

A ranar Laraba hukumar ta gayyaci sanatan kuma ya amsa gayyatar ranar Alhamis inda ya sha tambayoyi har sai da ya kwana a ofishin yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel