Bidyo: Yadda wani karamin jami’an tsaro ya hana Alkalin Alkalai shiga kotu

Bidyo: Yadda wani karamin jami’an tsaro ya hana Alkalin Alkalai shiga kotu

Wani jami’in hukumar tsaro ta farin kaya, Civil Defence ya hana babban alkaliyar jahar Kebbi, kuma shugaban Alkalan jahar dake rike da rikon mukamin Alkalin Alkalan jahar, Elizabeth Karatu daga shiga kotu a ranar Alhamis din data gabata.

Hakan ya bayyana ne cikin wani bidiyo dake yawo a kafafen sadarwar zamani, inda aka hangi jami’in da kuma dogarin Elizabeth, wanda shima jami’in Dansanda ne suna cacar baki akan hana Elizabeth shiga kotu don ta yanke hukunci.

KU KARANTA: Allah Ya tona asirin matashin daya shahara wajen satar wayoyin salula a Masallatai

Duk kokarin da Dansandan dogarin Alkaliyar ya yi na ganin ta samu shiga kotun domin ta yanke hukunci na karshe a wani shari’a dake gabanta, ya ci tura, sakamakon jami’in yace umarni aka bashi kada ya barta ta shiga kotu.

Dama dai akwai jikakkiya tsakanin Elizabeth da gwamnatin jahar, inda ta yi zargin gwamnan jahar ya ki tabbatar da ita a matsayin Alkalin Alkalan jahar Kebbi saboda it aba Musulma bace, duk da cewa majalisar dokokin jahar ta tabbatar da cancancarta.

Rashin tabbatar da ita wannan mukami ne ya kawo rikici tsakanin gwamnati da ita, wanda har ta kai ga ta kai karar gwamnan jahar ga majalisar sharia ta koli, amma duk da sanya baki da majalisar ta yi Gwamna Bagudu bai tabbatar da ita ba.

Da yake tsokaci game da bidiyon, shugaban kungiyar lauyoyi reshen jahar Kebbi, Husseini Zakariya ya bayyana cewa ya kalli bidiyon, kuma zasu kafa kwamitin bincike domin gudanar da cikakken bincike game da lamarin tare da gano musabbabin aukuwar lamarin.

Sai dai shugaban hukumar NSCDC, Abdullahi Muhammad Gana ya bayyana cewa jami’insu bai yi wani laifi daya hana Elizabeth shiga kotu ba, domin a cewarsa kotun a garkame yake a lokacin, don haka aikinsa yake yi a wannan lokaci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel