Shugaba Buhari ya dawo Abuja bayan taron AU

Shugaba Buhari ya dawo Abuja bayan taron AU

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli bayan ya halarci taron kungiyar kasashen Afrika na 12 a Niamey, jumhuriyar Nijar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa jirgin Shugaban kasar, wanda ke dauke da shugaba Buhari da wasu mukarrabansa ya isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja da misalin karfe 1:25 na rana.

Yayinda yake a kasar Nijar, Najeriya da Kasar Benin sun rattaba hannu a kan wata muhimmiyar yarjejeniya kulla kasuwanci a gaban shugabannin kasashe a dake halartar taron shugabannin kasashen Afrika (AU) da ake yi a ranar, Lahadi.

An tafa wa shugaba Buhari, da takwaransa na kasar Benin, Patrice Talon, a yayin da suka sa hannu a kan takardun kulla yarjejeniyar a taron da ke kan gudana a birnin Niamey, hedikwatar jamhuriyar Nijar, inda kuma za a kafa hedikwatar cibiyar kasuwanci da yarjejeniyar ta samar.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta ceto manoma 13 daga hannun masu garkuwa da mutane a Kaduna (hotuna)

Najeriya ce kasar Afrika ta 53 da ta saka hannu a kan yarjejeniyar kasuwancin. Shugaba Buhari ya amince da shiga tsarin yarjejeniyar kasuwanci maras shinge bayan kwamitin da ya kafa domin nazarin tsarin ya mika masa rahotonsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel