Buba Galadima ya fadi dalilin sa na juyawa Buhari baya

Buba Galadima ya fadi dalilin sa na juyawa Buhari baya

Alhaji Buba Galadima, tsohon na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin 8, ga watan Yuli, ya bayyana a gaban kotun daukaka karar zaben shugaban kasa dake zaman ta a garin Abuja domin bayar da shaida.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Alhaji Buba Galadima yayin bayar da shaida ya kuma ya kuma zayyana dalilan sa na juya wa shugaba Buhari baya tare da goyon bayan dan takarar kujerar shugaban kasa na zaben bana a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar.

A yayin wannan shi ne karo na farko da Alhaji Buba ya bayyana a gaban kotun a matsayin mai bayar da shaida na tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku, ya kuma fayyace zare da abawa na dalilan juya wa Buhari baya a yayin babban zaben kasa na bana.

Cikin shaidar da ya gabatar, Alhaji Buba ya shaidawa kotun cewa, ya dawo daga rakiyar shugaban kasa Buhari a sanadiyar rashin adalci da ya zamto al'ada a gwamnatin sa da kuma gazawar sa wajen tabbatr da aminci a kasar nan.

KARANTA KUMA: Buhari ya sha alwashin goyon bayan tabbatar da martabar tsaro da siyasa a kasar Libiya

Duk da goyon bayan shugaba Buhari a manyan zabukan kasa na 2003, 2007, 2011 da kuma na 2015, Buba Galadima ya ce a halin yanzu ya sauya sheka sakamakon gazawar tsohon amininsa na cika alkawurran da ya daukar wa al'ummar Najeriya yayin yakin neman zabe.

A yayin da ya ci gaba tarayyar gida da Buhari a karkashin inuwar jam'iyya ta APC, Alhaji Buba yayin amsa tambayar Lauya Wole Olanipekun, ya musanta zargin cewa fushin rashin samun nadin mukamin minista bayan samun nasara a 2015 bai sanya ya juya wa amininsa baya ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel