Hajjin bana: Hukumar NAHCON ta nada jami’an kula da kowane masaukin Alhazai

Hajjin bana: Hukumar NAHCON ta nada jami’an kula da kowane masaukin Alhazai

Hukumar da ke kula da jigilar alhazai ta kasa (NAHCON), ta nada jami’an da za su kula da kowane masauki da za ta saukar da maniyyatan kasar a birnin Madina.

Babban Jami’in Kula da AlhazanNajeriya a Madina, kuma Sakataren Riko na NAHCON, Ahmad Maigari ne ya bayyana hakan a lokacin da ya gudanar da taro da masu ruwa da tsaki wajen samar da mazaukai a Madina. NAHCON baki daya a lokutan gudanar da aikin ziyara a Madina.

Ya kara da cewa wannan sabon tsari zai kuma kara samar da hanyoyin sadarwa da tuntubar juna ga daukacin masaukan Alhazan Najeriya da kuma kan su ma’aikatan da jami’an NAHCON baki daya a lokutan gudanar da aikin ziyara a Madina.

Kamar yadda tsarin tafiya aikin Hajji ya ke, wadanda aka fara jigila daga farko-farko, su na zarcewa ne Madina su fara yin kwanakin ziyarce-ziyarce a can, kafin a wuce da su Makka.

Bayan kammala aikin Hajji kuma, sai a dibe su daga Makka zuwa filin jirgin Jedda, domin maido su gida Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: An samu rabuwar kai a tsakanin gwamnonin PDP

Maigari ya ce an gudanar da taron ne tare da masu mazaukan bakin domin tabbatar da cewa an samu hanyoyi nagari wajen kula da jin dadin Alhazan Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel