Buhari ya sha alwashin goyon bayan tabbatar da martabar tsaro da siyasa a kasar Libiya

Buhari ya sha alwashin goyon bayan tabbatar da martabar tsaro da siyasa a kasar Libiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa Najeriya ba za ta gushe ba wajen ci gaba da goyon bayan tabbatar da dawo da martaba da kuma aminci na tsaro da siyasa a kasar Libiya dake Arewacin nahiyyar Afirka.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai na fadar Villa dake garin Abuja a ranar Litinin 8, ga watan Yulin 2019.

Hadimin shugaban kasar ya bayyana cewa, ubangidan sa ya sha wannan alwashi yayin ganawa da shugaban hadin kan kasa na gwamnatin kasar Libiya, Fayez Al-Sarraj, a wani bigire na daban yayin taron kungiyar kasashen Afirka na AU da aka gudanar a ranar Lahadi cikin birnin Niamey na kasar Nijar.

Cikin kalami na sa kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, shugaba Buhari ya ce Najeriya za tayi iyaka bakin kokarin ta wajen taimakawa kasar Libiya dawo da martabar ta da kuma aminci.

KARANTA KUMA: Jihar Bayelsa ba za ta bari wanda babu Allah a zuciyar sa ya mulke ta ba - Dickson

Ganawar Buhari da ta gudana akan batutuwan dangartakar dake tsakanin Najeriya da kuma kasar Libiya tare da Al-Sarraj. Buhari ya ce a halin yanzu akwai kimanin 'yan asalin kasar Najeriya 6000 dake kasar Libiya masu neman hanyar ketarewa zuwa nahiyyar Turai.

A wani rahoton mai nasaba da wannan jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban kasa Buhari yayin taron na AU ya mika kokon barar neman agajin babban bankin ci gaban addinin Islama na duniya, Islamic Development Bank, a kan habaka ci gaban gine-gine a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel