Hana sa hijabi: Iyayen dalibai Musulmi sun gargadi shugabar makarantar sakandare na ISI

Hana sa hijabi: Iyayen dalibai Musulmi sun gargadi shugabar makarantar sakandare na ISI

Ana ci gaba fafatawa tsakanin iyaye da hukumar makarantar sakandare na jami’ar Ibadan akan batun hana yara mata dalibai sanya hijabi.

A yanzu haka iyayen dalibai mata Musulmi na makarantar mai suna International School Ibadan (ISI), sun zargi shugabar makarantar Misis Phebean Olowe da laifin rura wutar wani rikici a cikin makarantar ta hanyar kuntata wa dalibai mata Musulmi masu neman a bar su suna saka hijabi a cikin makarantar.

Kungiyar Iyayen Dalibai Musulmin na ISI ce ta yi wannan zargi a ranar Asabar a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Iyayen daliban sun yi ikirarin cewa hukumar makarantar na muzanta wa dalibai mata Musulmi masu zuwa makarantar sanye da hijabi.

Tun a cikin watan Nuwamba, 2018 ne batun sanya hijabi ya zama rikici a makarantar, har ta kai ga kungiyar iyayen dalibai mata musulmi suka maka makarantar, Jami’ar Ibadan da kuma Hukumar Gudanarwar makarantar kotu.

Amma kuma a ranar 26 Ga Yuni, sai Babbar Kotun Jihar Oyo ta kori karar, a bisa dalilin cewa wadanda suka kai karar ba su da hurumin kai kara a kungiyance.

Sai kuma a ranar Alhamis da ta gabata ne wani wanda ‘yar sa ke karatu a makarantar, mai suna Idris Badiru, ya zargi Shugabar Makarantar Misis Olowe da Akantan makarantar Mista Odewale da wasu malaman makarantar da cewa sun ci zarafin ‘yar sa Ikhlas Badiru.

Badiru ya ce duka da kotu ta ce kungiya ba ta da ‘yancin kai kara, bai yiwuwa a hana ‘yar sa ‘yancin ta na yin shigar hijabi a makaranta. Ya kuma bayyana cewa a gabansa haka hana yar tasa shiga makaranta sanye da hijabi.

KU KARANTA KUMA: Ka nada jajirtattun yan jam’iyya kadai a matsayin ministoci – APC reshen Enugu

Shugaban Kungiyar Iyayen Dalibai Musulmi na sakandaren ISI, Abdur-Rahman Balogun, ya gargadi shugabar makarantar da kada ta kuskura ta haddasa rikici a makarantar.

Sai dai kuma shugabar makarantar ta ki yin tsokaci akan lamarin, domin a lokacin da aka tuntube ta kan lamarin sai ta kashe wayarta kamar yadda majiyarmu ta Premium Times ta ruwaito.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel