Ka nada jajirtattun yan jam’iyya kadai a matsayin ministoci – APC reshen Enugu

Ka nada jajirtattun yan jam’iyya kadai a matsayin ministoci – APC reshen Enugu

Gabannin kafa sabuwar majalisar tarayya, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Enugu ta shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhariu da ya nada jajirtattun mambobin jam’iyyar kadai a matsayin ministoci.

Jam’iyyar reshen jihar ta ce lallai ya zama dole Buhari ya janye daga duk wani kudiri na son kawo wadanda ke son yin girbi a wajen da basu yi shuka ba, ko kuma ministocin da ba za su taimaka wajen ci gaban jam’iyyar ba a jihohinsu kamar yadda aka fuskanta a baya.

Shugaban APC a jihar Enugu, Dr. Ben Nwoye, wanda yayi Magana a karshen mako bayan wani taron shugabannin jam’iyyar a jihar wanda aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Enugu, ya bayyana cewa rassan jam’iyyar na jihohi a fadin kasar sun fuskanci babban kalubale a mulkin Buhari na farko saboda zargin nadin wadanda ba asalin mambobin jam’iyyar bane a matsayin ministoci da sauran many mukaman gwamnati.

APC reshen Enugu ta kara da cewa ba wadanda basu yi amanna da APC da ajandar Next Level a Shugaban kasa ba mukami zai kawo cikas musamman a matakin jiha.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Karo na farko Oshiomhole ya bayyana a kotun zaben Shugaban kasa

Har ila yau, tayi kira ga Shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole da kwamitin masu gudanarwa da su yi adalci sannan su janye dakatarwar da suka yi ma jiga-jiganta a jihar akan zargin saba ma jam’iyya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel