Jihar Bayelsa ba za ta bari wanda babu Allah a zuciyar sa ya mulke ta ba - Dickson

Jihar Bayelsa ba za ta bari wanda babu Allah a zuciyar sa ya mulke ta ba - Dickson

Honarabul Seriake Dickson, gwamnan jihar Bayelsa, ya ce al'ummar jihar sa ba za su taba zaben wanda babu barbarshin imani ko kuma Allah a zuciyar sa a matsayin wanda zai ci gajiyar kujerar sa ta gwamna.

Cikin jawaban da ya gabatar yayin kammala taron addu'o'i da kuma azumi na kwanaki uku da aka gudanar dangane da gabotowar zaben gwamnan jihar a ranar 16 ga watan Nuwamba, gwamnan Dickson ya ce dole magajin kujerar sa ya kasance mai tsarkakakken imani.

Jaridar This Day ta ruwaito cewa, an gudanar da wannan gagarumin taro a cibiyar Ecumenical dake birnin Yenagoa na jihar Bayelsa.

A jawabin da mai magana da yawun gwamnan Fidelis Soriwei ya gabatar, ubangidan sa ya dukufa wajen ganin magajin kujerar sa ya kasance mai sanya Allah a gaba cikin al'amurra sabanin mai hankoron kujerar ta kowane hali.

A cewar gwamna Dickson, jihar Bayelsa ba za ta sake kasancewa karkashin jagorancin miyagun ababe na kaucewa hanya irin su tsubbace-tsubbace, zubar jinin al'umma, da kuma tayar da zaune tsaye.

KARANTA KUMA: Buhari ya yi barar inganta gine-ginen Najeriya a taron AU

Gwamnan ya kirayi al'ummar jihar Bayelsa da su kauracewa shiga sabgogi da kuma ababe na kungiyoyin asiri, wajen yaudarar su cikin afkawa halaka domin cikar burace-buracen siyasa.

Dickson ya kara da cewa, magajin kujerar sa zai kasance zakakurin gaske kuma mai akidar tabbatar da ci gaban tsare-tsare da kuma manufofin dimokuradiya na jam'iyyar PDP.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel