Buhari ya yi barar inganta gine-ginen Najeriya a taron AU

Buhari ya yi barar inganta gine-ginen Najeriya a taron AU

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, domin neman agaji ya mika kokon bara ga babban bankin ci gaban musulunci na duniya a kan shawo kan matsalar rashin ingantattun gine-gine a kasar nan.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa kamar yadda jaridar The Punch ta rruwaito.

Adesina ya bayar da shaidar cewam shugaban kasa Buhari ya yi wannan kira na neman agaji yayin ganawa da mataimakin shugaban bankin ci gaban addinin Islama na duniya, Dakta Mansur Mukhtar, a wani bigire na daban yayin taron kungiyar kasashen Afirka da aka gudanar a birnin Niamey na kasar Nijar.

Kamar yadda shugaban kasa Buhari yayi ikirari, ba bu wani adadin kudi da zai wadatar da ci gaban Najeriya wajen samar da gine-gine tare da inganta su a yayin da adadin al'ummar kasar nan ke ci gaba da tumfayawa.

KARANTA KUMA: Wani mutum ya kashe budurwar sa bayan ya sha kwayar Tramadol

Shugaban kasa Buhari ya kuma yi jinjina tare da godiya mai tarin gaske ga babban bankin na duniya musamman wajen bayar da gudunmuwar ci gaban kasar nan a fannin noma, kasuwanci, hannun jari da kuma raya karkara.

Cikin na sa jawaban, mataimakin shugaban bankin ci gaban musulunci na duniya, Dakta Mansur, ya yabawa shugaban kasa Buhari da kuma Najeriya dangane da rattaba hannu kan amincewa da yarjejeniyar kasuwanci na bai daya a nahiyyar Afirka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel